DSS Ta Titsiye Sakataren Gwamnatin Jihar Ogun Kan Babban Zaben 2023
- Hukumar DSS ta fara bincikar sakataren gwamnatin jihar Ogun, Tokunbo Talabi, na hannun daman gwamna Dapo Abiodun
- Jami'ai sun titsiye Talabi ne bisa zargin hannu a buga takardun zabe lokacin zaɓen 2023 da kuma badaƙalar kuɗin COVID19
- An tsare babban jami'in gwamnatin Ogun na tsawon sa'o'i 5 ranar Jumu'a, 4 ga watan Agusta, 2023 amma daga bisani ya shaƙi iskar yanci
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ogun state - Hukumar jami'an tsaron sirri na farin kaya (DSS) ta titsiye sakataren gwamnatin jihar Ogun, Tokunbo Talabi, kan wasu tuhume-tuhume almundahana da ake masa.
Jaridar Punch ta tattaro cewa DSS ta gayyaci sakataren kana daga bisani ta tasa shi da tambayoyi sakamakon ƙorafe-korafe da zargin da ake masa.
Wata majiya ta bayyana cewa jami'an DSS sun tsare SSG ɗin ne a hedkwatar hukumar da ke Oke-Mosan a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun ranar Jumu'a da ƙarfe 6:55 na magriba.
Matawalle, El-Rufai Da Tsofaffin Gwamnonin 3 Da Sunayensu Ya Fito Cikin Ministocin Tinubu Kashi Na Biyu
Rahoto ya nuna cewa jami'an hukumar sun tsare Mista Tolabi na tsawon awanni 5 a ranar Jumu'a amma daga bisani suka sake shi saboda kasancewarsa wanda aka sani.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Meyasa DSS take bincikar SSG na Ogun?
Idan baku manta ba ƙungiyar marubuta masu gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan adam (HURIWA) ta shigar da ƙorafi kan Sakataren ga hukumar yaƙi da cin hanci (EFCC).
Ƙungiyar ta buƙaci hukumar EFCC ta gudanar da bincike mai zurfi kan Mista Talabi da kuma kamfaninsa na buga takardu.
HURIWA na zargin sakataren da kamfaninsa sun buga takardun zaɓe na bogi kuma suka yi amfani da su wajen maguɗin zaɓen gwamna ranar 18 ga watan Maris.
A rahoton PM News, wata majiya ta ce daga cikin batutuwan da aka tado yayin tambayoyi ga Sakataren shi ne rawar da kamfaninsa ya taka a ruɗanin tallafin korona.
Haka zalika DSS ta tambayi Talabi game da alaƙar kamfaninsa da wasu maƙudan kudaɗe na jihar Ogun da kuma rawar da ya taka a zaben 2023.
Bazoum: Hambararren Shugban Nijar Ya Roki Amurka da Wasu Kasahse Su Kai Masa Ɗauki
A wani rahoton kuma Muhammed Bazoum, shugaban Nijar da sojoji suka kifar ya aike da sako ga Amurka da sauran ƙasashen duniya.
Bazoum ya yi gargaɗin cewa sakamakon da zai biyo baya ba zai yi kyau ba ga Nijar da sauran ƙasashen Afirka matuƙar sojoji suka yi nasara a Nijar.
Asali: Legit.ng