Yan Sanda Sun Daƙile Yan Bindiga a Caji Ofis, Sun Cafke Imfoma a Zamfara

Yan Sanda Sun Daƙile Yan Bindiga a Caji Ofis, Sun Cafke Imfoma a Zamfara

  • Dakarun 'yan sanda sun yi nasarar daƙile yunkurin 'yan bindiga na kai hari caji ofis ɗin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara
  • Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan Zamfara ya ce bayan artabu da maharan, yan sanda sun kama wata Imfoma
  • Matar yar kimanin shekara 35 a duniya ta amsa laifinta kuma an ga lambobin yan bindiga a wayoyinta guda biyu

Zamfara - Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce jami’anta sun fatattaki ‘yan bindiga da suka kai hari a ofishin ‘yan sanda na karamar hukumar Zurmi.

Rundunar ta ce ta kuma kama wata mata mai shekaru 35 da ake zargi da bayar da bayanai ga yan ta'adda watau imfoma, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Jami'an hukumar yan sanda a bakin aiki.
Yan Sanda Sun Daƙile Yan Bindiga a Caji Ofis, Sun Cafke Imfoma a Zamfara Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Yazid Abubakar ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wani taron manema labarai a Gusau.

Kara karanta wannan

Dakarun Soji Sun Kai Farmaki Sansanin 'Yan Ta'adda a Cikin Daji, Sun Samu Gagarumar Nasara

Abubakar ya ce jami’an ‘yan sandan da ke aiki a Caji Ofis din sun samu sahihan bayanan sirri da ke cewa wasu gungun ‘yan bindiga na shirin kai harin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Jami’an ‘yan sanda sun hada kai wuri guda, suka tunkari ‘yan bindigan inda suka yi ta artabu wanda ya dauki tsawon sa’o’i ana musayar wuta."
“Sakamakon haka, sun kashe daya daga cikin ‘yan bindigar yayin da sauran suka tsere zuwa cikin daji suna zubar da jini a kan hanya saboda raunukan da suka samu."
“Binciken da ‘yan sanda suka yi bayan faruwar lamarin, sun kama wata mata ‘yar shekara 35 da ake zargin imfoma ce daga kauyen Rukudawa."

Matar da aka kama ta fasa kwai

Kakakin yan sandan ya ƙara da bayanin cewa matar ta amsa laifinta kuma an samu lambobin yan bindiga a wayar da ke hannunta.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Ƙara Yi Wa Mutane 10 Yankan Rago a Arewacin Najeriya

Tribune ta rahoton Abubakar na cewa:

"Matar da ake zargin ta amsa cewa tana aiki da ƙasurgumin ‘yan fashin dajin nan, Dankarami Gwaska, a matsayin mai masa leƙen asiri kuma ya ba ta aikin sa ido a ofishin ‘yan sanda."
“An kwato wayar hannu guda biyu dauke da lambobin wayar ‘yan bindiga daga hannunta."

Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Gona Sanata a Jihar Kwara, Sun Halaka Manaja

A wani labarin kuma Wasu yan bindiga da ake kyautata zato masu garkuwa da mutane ne sun kai hari gidan gonar tsohon Sanatan Kwara ta kudu.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun halaka Manajan da ke kula da gidan gonan kuma ɗan uwan tsohon Sanatan yayin harin na ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262