Gwamna Idirs Ya Tura Tawaga Zuwa Jamhuriyar Benin Kan Yan Kebbi 10 da Aka Kama

Gwamna Idirs Ya Tura Tawaga Zuwa Jamhuriyar Benin Kan Yan Kebbi 10 da Aka Kama

  • Gwamna Nasiru Idris na jihar Kebbi ya tada tawagar wakilai zuwa jamhuriyar Benin domin kubutar da wasu 'yan jihar da aka kama
  • Rahoto ya nuna jami'an tsaron Benin sun cafke matasa 10 yan asalin Kebbi bisa zargin alaƙa da ƙungiyar Boko Haram
  • Tawagar wakilai da gwamnan ya tura zata yi duk mai yiwuwa bisa tanadin doka wajen kuɓutar da mutanen

Kebbi state - Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Nasiru Idris, ya aike da tawaga zuwa jamhuriyar Benin domin kai daukin sako wasu ‘yan asalin jihar su 10 da aka kama.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jami'an tsaron Jamhuriyar Benin sun cafke mutanen su 10 'yan asalin jihar Kebbi a Najeriya kana suka tsare su a Magarkama.

Gwamna Nasiru Idris na jihar Kebbi.
Gwamna Idirs Ya Tura Tawaga Zuwa Jamhuriyar Benin Kan Yan Kebbi 10 da Aka Kama Hoto: Governor Nasiru Idris
Asali: UGC

Matasan 10 da jami'an tsaron Benin suka kama sun haɗa da, Yusha’u Mohammed (38), Surajo Likita (25), Suleiman Usman (25), Ibrahim Umar (29), Nazifi Tahiru (18), Babangida Aliu (30), da Usama Kabiru (25).

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwan Sani 7 Dangane Da Abdullahi Umar Ganduje, Sabon Shugaban APC Na Kasa

Sauran sun ƙunshi Babawo Mohammed (35), Hamisu Dan Ashibi (25) da kuma Ibrahim Rilwanu (25) dukkansu yan asalin ƙaramar hukumar Dandi a jihar Kebbi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoto ya nuna suna hanyar komawa gida ne daga Benin a ranar Alhamis 1 ga watan Yuni lokacin da jami’an tsaron kasar suka kama su a kauyen Kaini Tunga na Jamhuriyar Benin.

Meyasa jami'an tsaro suka kama matasan?

Gwamnatin Kebbi ta bayyana cewa jami'an tsaron Benin sun laƙaba musu laifin cewa suna cikin, "mayaƙan ƙungiyar ta'addancin nan Boko Haram."

Ta ƙara da bayanin cewa ta tsiya, jami'ai suka kwace musu wayoyi, kudaɗe da sauran kayayyakin da ke tattare da su.

Rahoton ya ce ana tsare da su a wani wuri da ba a faɗi sunansa ba a birnin Cotonou na Jamhuriyar Benin, kuma duk kokarin gano su ya ci tura.

Kara karanta wannan

Matawalle, El-Rufai Da Tsofaffin Gwamnonin 3 Da Sunayensu Ya Fito Cikin Ministocin Tinubu Kashi Na Biyu

Nauyin da gwamna ya ɗora wa tawagar

Tawagar gwamnatin tana ƙarƙashin jagorancin mai bai wa gwamna shawara ta musamman kan ayyuka na musamman, Shafiu Abubakar.

Tuni dai suka gana da jakadan Najeriya a jamhuriyar Benin tare da mikawa jakadan takardar neman sa hannun sa wajen ganin an sako ‘yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba.

Gwamna Idris ya bukaci tawagar da ta binciki duk wata hanyar da doka ta tanada domin ceto wadanda abin ya shafa tare da dukiyoyinsu, rahotanni sun tabbatar.

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ta Amince da Nadin Kwamishinoni 18

A wani rahoton kuma Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tantance tare da tabbatar da naɗin sabbin kwamishinoni 18 da gwamna Dauda Lawal ya aiko mata.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na majalisar, Malam Nasiru Biyabiki ya fitar a Gusau ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262