Juyin Mulki: Hukumar Shige Da Fice Ta Gargadi 'Yan Najeriya Kan Tafiye-Tafiye Zuwa Nijar
- Hukumar kula da shige da fice ta gargaɗi 'yan Najeriya kan zuwa jamhuriyar Nijar biyo bayan juyin mulkin da aka yi
- Kwanturolan da ke kula da iyaka ta musamman ta Jibia da ke jihar Katsina, Mustapha Sani ne ya yi gargadin ga ‘yan Najeriya
- Ana ƙara samun fargaba tun bayan juyin mulkin a inda ƙungiyar ECOWAS ta sanayawa Nijar takunkumi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Katsina - Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya (NIS), ta gargaɗi 'yan Najeriya kan zuwa jamhuriyar Nijar biyo bayan hamɓarar da gwamnantin Bazoum da sojoji suka yi.
Kwanturolan da ke kula da iyakar yankin Jibia da ke jihar Katsina, Mustapha Sani ne ya yi gargaɗin ga 'yan Najeriya a yayin bikin cikar hukumar shekaru 60 da kafuwa kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
An bukaci 'yan Najeriya su yi zamansu a gida
Sani ya nemi 'yan Najeriya da su yi zamansu a cikin gida Najeriya maimakon ƙoƙarin haurawa zuwa jamhuriyar Nijar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce za su kama duk wanda suka gani yana ƙoƙarin tsallakawa zuwa Nijar sannan su dawo da shi gida.
Ya ƙara da cewa, jami'ansu za su ci gaba da tsare duk wasu hanyoyi har zuwa lokacin da za a ɗage takunkumin.
An jibge jami'ai domin killace iyakar Najeriya da Nijar
Sani ya bayyana cewa yanzu haka an jibge jami'an hukumar ta kula da shige da ficen domin tare mutanen da ka iya shigowa Najeriya daga Nijar ta ɓarauniyar hanya.
Ya ce duk da abubuwa da dama da 'yan Najeriya suka haɗa da 'yan Nijar kamar irinsu addini da al'adu, hakan ba zai ba su damar shigowa ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.
A rahoton na Channels TV, Sani a ƙara da cewa, yanzu haka sun tura jami'ansu zuwa duk inda wata ɓarauniyar hanya da ake bi a shigo Najeriya ta ita take domin rufe ta.
Atiku ya yi magana kan abinda ke faruwa a Nijar
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan tsokacin da ɗan takarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya yi dangane da juyin mulkin da aka yi a Nijar.
Atiku ya ba da shawarar cewa matakai na diflomasiyya ya kamata ECOWAS ta ɗauka ba wai amfani da ƙarfin soji ba.
Asali: Legit.ng