Gwamnan Benue Ya Gana da Shettima Kan Batun Samar da Isasshen Abinci
- Gwamnan jihar Benuwai ya gana da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima a Aso Villa ranar Alhamis
- Hyacinth Alia ya yi kus-kus da Shettima ne kan batun samar da wadataccen abinci a Najeriya
- Ya kuma yaba da naɗa tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai, a ranar Alhamis ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ba da fifiko wajen bunkasa harkar noma domin taimaka wa Najeriya ta samu wadatar abinci.
Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai na gidan gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan gana wa da ta gudana a fadar shugaban ƙasa ta zo ne jim kaɗan bayan sun halarci taron majalisar zartarwan APC ta ƙasa (NEC).
A jawabinsa bayan gana wa da Shettima, gwamna Alia ya ce mataimakin shugaban ƙasa yana da kwarewa da kwarin guiwa a harkar noma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bisa haka ya buƙaci Shettima ya goyi bayan gwamnatin jihar Benuwai a matsayin cibiyar abinci domin samar da wadataccen abinci ga jihar da ƙasa baki ɗaya.
A wani binciken abinci da kaya masu gina jiki da aka gudanar a wannan shekarar, ya nuna kusan 'yan Najeriya miliyan 25 ke fuskantar barazanar yunwa saboda ƙarancin abinci.
Gwamnan ya yaba da naɗa Ganduje shugaban APC
Haka zalika, gwamna Alia na jihar Benuwai ya yi tsokaci kan zaben tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban APC ta ƙasa.
Alia ya nuna jin daɗinsa da gamsuwa da naɗa Ganduje a wannan matsayi da sauran shugabannin jam'iyya mai mulki, wanda NEC ta yi a taronta na ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa Ganduje a matsayinsa na mai kishin kasa zai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu wajen hada kan Najeriya ta hanyar cika alkawarin da ya yi, Sunnews ta tattaro.
Gwamnatin Kano Ta Kama Uba Dansa Bisa Zargin Wawure Biliyan N4bn
A wani rahoton kuma Gwamnatin Kano ta hannun hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar ta bankaɗo badakalar sace biliyan N4.
Hukumar PCACC karkashin Muhyi Rimin Gado ta kama uba da ɗansa da ake zargi da hannu a wawure kuɗin mallakin gwamnati.
Asali: Legit.ng