Gwamnatin Kano Ta Kama Uba Dansa Bisa Zargin Wawure Biliyan N4bn

Gwamnatin Kano Ta Kama Uba Dansa Bisa Zargin Wawure Biliyan N4bn

  • Gwamnatin Kano ta hannun hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar ta bankaɗo badakalar sace biliyan N4
  • Hukumar PCACC karkashin Muhyi Rimin Gado ta kama uba da ɗansa da ake zargi da hannu a wawure kuɗin mallakin gwamnati
  • Ta ce nan ba da jima wa ba zata gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban Kotu domin a hukunta su daidai da abinda suka aikata

Kano - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC), ta ce ta kama babban wanda ake zargi da karkatar da sama da Naira biliyan 4 mallakar gwamnatin jihar.

Wanda ake zargin shi ne ya kafa ƙungiya mai zaman kanta (NGO) mai suna "Association of Compassionate Friends" kuma sa hannunsa ne a asusun bankin kamfanin 'Limestone Processing Link'.

Shugaban PCACC, Muhyi Rimin Gado.
Gwamnatin Kano Ta Kama Uba Dansa Bisa Zargin Wawure Biliyan N4bn Hoto: dailynigerian
Asali: UGC

Hukumar PCACC karkashin gwamnatin Abba Gida-Gida ce ta sanar da bankaɗo wannan badaƙala ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta, 2023, jaridar Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan Taro a Aso Villa, NLC Ta Yi Magana Kan Janye Zanga-Zanga da Shiga Yajin Aikin da Ta Shirya a Najeriya

Ta ƙara da bayanin cewa waɗanda suka wawure makudan kuɗin sun yi amfani da Asusun kamfanin da kuma na ƙungiyar NGO wajen karkatar da N4bn.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda aka kama wanda ake zargi?

Haka zalika hukumar ta bayyana cewa ta yi nasarar cafke wanda ake zargin ne bayan ya kutsa cikin gingimemen ɗakin ajiyan da gwamnati ta ƙwace.

A cewarta, wannan abu da ya aikata ya saɓa wa dokar yaƙi da cin hanci da rashawa ta 2008.

Sanarwan hukumar ta yi bayanin cewa PCACC ta kwace tare da rufe wuraren ajiyar kayayyakin bisa umarnin kotu.

"Rufe manyan shagunan na da alaƙa da almundahanar karkatar da kudaden jihar Kano sama da Naira biliyan 4, wanda aka biya a matsayin tallafi ga kamfanin inganta noma na Kano," in ji ta.
"Har ila yau, akwai dan wanda ake zargin a tsare, wanda ke da hannu a asusun ajiyar banki na kungiyar, wanda aka yi amfani da shi wajen wawure biliyan 3.27."

Kara karanta wannan

Cikin Tsohon Gwamnan PDP Ya Duri Ruwa Bayan Kotu Ta Umarci Ya Yi Bayanin Yadda Ya Kashe N200bn Na Bangaren Ilmi a Jiharsa

Hukumar PCACC ta ce an yi amfani da Naira miliyan 400 daga cikin kudin wajen bude wani asusun ajiya da sunan babban wanda ake zargin.

Ta kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Fani-Kayode Ya Yi Magana Bayan Rashin Ganin Sunansa a Ministoci, Ya Fadi Mataki Na Gaba

A wani rahoton kuma Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya ayyana jerin ministocin da shugaban ƙasa ya naɗa a matsayin zaɓi na gari.

Haka nan kuma, Festus Keyamo, tsohon ministan kwadugo ya yaba da ministocin duk da ba bu sunansa a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262