Kotu Ta Tura Shugabar Masu Addinin Gargajiya, Iya Osun Gidan Yari Saboda Cin Mutuncin Malamin Islama a Ilorin
- Ana samun karuwar yawaitar rikice-rikice a tsakanin malaman addinin Musulunci da na gargajiya a Ilorin
- Kotu ta ba da umarnin tsare wata shugabar masu addinin gargajiya, Madam Efunsetan Abebi Aniwura Olorisha a gidan yari
- Hakan ya samo asali ne daga korafin da wani malamin Musulunci ya shigar kan zargin bata ma sa suna da ta yi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ilorin, jihar Kwara - Wata kotun majistare da ke zama a Ilorin, jihar Kwara, ta yanke hukuncin tsare Madam Efunsetan Abebi Aniwura Olorisha a gidan yari na Oke-Kura.
Madam Abebi, wacce aka fi kira da Iya Osun, ta kasance babbar mamba a ƙungiyar masu addinin gargajiya na Isese da ke jihar Kwara.
Kotu ta tsare Iya Osun bisa zargin ƙazafi ga malamin addini a Ilorin
Bayanan da Legit.ng ta samu sun nuna cewa, an hana bayar da belin matar, wacce ita ce shugabar masu addinin gargajiya na Isese a ranar 1 ga watan Agusta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan dai na da alaƙa da ƙorafi kan ɓata suna da wani shehin malamin addinin Muslunci Sheikh Okutagidi, tare da wasu Musulmai da ke Illorin suka shigar.
Haka nan kotun ta bayar da umarnin tsare wani makanike Oba Olowu, wanda shi ne ya naɗi bidiyon ƙazafin da Iya Osun ɗin ta yi wa malamin.
Kotun ta ƙi yarda da bayar da belinsu, inda ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar Talata, 29 ga watan Agusta.
Rikici ya yi ƙamari tsakanin mabiya addinin Islama da na Isese a Ilorin
A baya Legit.ng ta yi wani rahoto kan ɓarkewar rikici tsakanin mabiya addinin Muslunci da na gargajiya Isese a Ilorin, yayin da jami'an 'yan sanda suka kama shugabarsu, Madam Efunsetan Abebi Aniwura Olorisha, da ake kira da Iya Osun a ranar Litinin, 31 ga watan Yuli.
Iya Osun ta yi iƙirarin cewa, Sheikh Okutagidi ya nemi taimakonta wajen haihuwar ɗaya daga cikin 'ya'yansa kuma ta taimaka masa.
Yan bindiga sun halaka manajan gidan gonan sanatan jihar Kwara
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wasu 'yan bindiga da ake tunanin masu garkuwa da mutane ne da suka kai hari gidan gonar sanatan Kwara ta Kudu.
A yayin harin na su, sun halaka manajan da ke kula da gidan gonar wanda ya kasance ɗan uwan sanatan ne.
Asali: Legit.ng