Gwamnatin Tarayya Ta Maka Kungiyoyin Kwadago a Kotu Kan Zanga-Zanga

Gwamnatin Tarayya Ta Maka Kungiyoyin Kwadago a Kotu Kan Zanga-Zanga

  • An maka Kungiyoyin Kwadago na Najeriya a kotu a ranar Laraba 2 ga watan Agusta fara yajin aiki
  • Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta maka kungiyoyin kwadago na NLC da TUC saboda saba umurnin kotu na hana su zanga-zanga
  • Sai dai, akasin umurnin na kotu kungiyoyin kwadagon sun yi zanga-zanga a sassan Najeriya a ranar Laraba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi karar Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC, da Kungiyar Masu Sana'o'i, TUC, kan saba umurnin hana kungiyoyin kwadago yin yajin aiki da kotun masana'antu ta bada.

FG ta maka NLC da TUC a kotu

Gwamnatin Najeriya ta yi karar NLC da TUC a kotu
FG ta shigar da sabon kara kan NLC da TUC a kotu. Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

An shigar da karar na 'sanar da kotu saba umurninta' wanda aka saba da kira da 'form 48' a kotun masana'antu na kasa da ke Abuja a ranar Laraba, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaba Tinubu Ya Fada Mana a Aso Villa Inji Shugabannin ‘Yan Kwadago

A ranar Laraba, NLC ta ba wa gwamnatin tarayya wa'adin kwana bakwai ta janye dukkan tsare-tsarenta 'na musgunawa talakawa'.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma, gwamnatin tarayya ta ce kotun masana'antu ta bada umurni na hana kungiyoyin kwadago yin zanga-zanga ko yajin aiki kan batun janye tallafin man fetur.

Falana ya kare NLC da TUC

Sai dai Femi Falana, Lauya mai rajin kare hakkin bil adama, ya kare kungiyar, yana mai cewa yajin aikin ba ya nufin saba umurnin kotu kuma kungiyar na da daman yin zanga-zanga na lumana.

Amma Beatrice Jedy-Agba, babban lauya na tarayya, ta ce yajin aiki da zanga-zanga da aka shirya yi ba za a iya kiransa na lumana ba duba da cewa an yi su ne da munin "karya gwmnati da tada zaune tsaye, saka tsoro a zuciyar yan kasa."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Firai Ministan Canada Justin Trudeau Ya Saki Matarsa Bayan Shekaru 18

Kungiyar NLC Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Ranar 14 Ga Wata Idan FG Ba Ta Janye Karar Da Ta Shigar Ba

A bangare guda, kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan Agusta idan har Gwamnatin Tarayya ba ta janye karar da ta shigar da kungiyar ba.

Kungiyar ta bayyana haka ne yayin ganawar masu ruwa da tsaki na kungiyar a yau Alhamis 3 ga watan Agusta a Abuja.

Shugaban kungiyar, Joe Ajaero ya ce ma'aikatar shari'a da kotun masana'antu sun kaskantar da kansu ana amfani da su wurin lalata dimukradiyya, cewar Punch.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164