Juyin Mulki: ECOWAS Ta Aika Da Tawagar Sasanci Zuwa Jamhuriyar Nijar
- Kungiyar raya ƙasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), ta tura tawagar sasanci zuwa jamhuriyar Nijar
- Kungiyar ta tura tawagar wakilcin ne domin tattaunawa da sojojin da suka kifar da gwamnatin Bazoum
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wa'adin kwana bakwai da ECOWAS ta bai wa sojojin ke ƙaratowa
Abuja - Ƙungiyar raya ƙasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), ta tura tawagar sasanci zuwa jamhuriyar Nijar don tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin tsaron ƙasashen na ECOWAS ke gudanar da taro kan yadda za a ɓullowa lamarin Nijar ɗin a Abuja.
Kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da harkokin tsaro na ECOWAS, Abdel-Fatau Musah ne ya shaidawa manema labarai hakan a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
ECOWAS ta sanyawa Nijar takunkumi
A ranar Lahadin da ta gabata ne ƙungiyar ta ECOWAS ta sanyawa ƙasar ta Nijar takunkumi, inda ta bayyana cewa za ta iya amfani da ƙarfi wajen dawo da Bazoum da sojoji suka kifar.
Musah ya bayyana cewa amfani da ƙarfin na soji shi ne mataki na ƙarshe da ECOWAS za ta ɗauka idan ba a samu abinda ake so ta ruwan sanyi ba kamar yadda Reuters ta ruwaito.
Ya ƙara da cewa akwai buƙatar ECOWAS ta nuna cewa ba wai iya barazana ta iya ba, za ta iya ɗaukar matakan da suka dace.
Mutanen da ECOWAS ta tura sasanci da sojojin Nijar
Musah ya ƙara da cewa, Abdulsalami Abubakar, tsohon shugaban ƙasar Najeriya na mulkin soja ne ya jagoranci tawagar ta ECOWAS don tattaunawa da sojojin.
Shugaban masu tsaron hamɓararren shugaban ƙasa Janaral Abdourahmane Tchiani ne ke jagorantar ƙasar ta Nijar biyo bayan kifar da gwamnatin Bazoum da suka yi a ranar Laraba ta makon da ya gabata.
Ƙasashen duniya da dama sun yi Allah wadai da juyin mulkin na Nijar, musamman in aka yi la'akari da irin gudummawar da take bayarwa wajen yaƙi da kungiyoyin 'yan ta'adda.
Sojojin da ke jagorantar Nijar sun sanar da buɗe iyakokin ƙasar da ke tsakaninta da Algeria, Burkina Faso, Mali, Libya da Chad, waɗanda suka sanar da kullewa a baya kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
Fani-Kayode ya gargaɗi sojojin Mali, Burkina Faso da Nijar
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan gargaɗin da jigo a jam'iyyar APC, Femi Fani-Kayode ya yi ga ƙasashen da ke goyon bayan jamhuriyar Nijar.
Fani-Kayode ya ce Najeriya ba kanwar lasa ba ce, don haka ya yi kira ga ƙasar ta Nijar da ƙawayen na ta da su guji gwabza yaƙi da sojojin Najeriya.
Asali: Legit.ng