An Kara Samun Tsaiko a Shari'ar Ɗan China Da Ake Zargi da Kisan Ummita a Kano

An Kara Samun Tsaiko a Shari'ar Ɗan China Da Ake Zargi da Kisan Ummita a Kano

  • Sauraron karar babban zaben 2023 ya jawo an dakatar da zaman sauraron ƙarar kisan Ummita a jihar Kano
  • Ana zargin ɗan China mai suna Frank Geng Quanrong da halaka Ummita bayan wata 'yar taƙaddama ta shiga tsakaninsu
  • An dakatar da shari'ar ne saboda alkalin da ke sauraron ƙarar, Sunusi Ado Ma’aji, na cikin alkalan Kotu zaɓe a wata jiha

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano state - An sake gamuwa da sabuwar matsala a ci gaba da sauraron ƙarar kisan Ummulkulsum Sani Buhari wacce aka fi sani da Ummita a jihar Kano.

Ana zargin saurayin marigayya Ummita kuma ɗan asalin ƙasar China, Frank Geng Quanrong, da kashe budurwar, lamarin da ya tada ƙura a sassan ƙasar nan.

Karar kisan Ummita da ake zargin Ɗan China da aikatawa.
An Kara Samun Tsaiko a Shari'ar Ɗan China Da Ake Zargi da Kisan Ummita a Kano Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Jaridar Aminiya ta tattaro cewa tun a ranar 6 ga watan Afrilu ya kamata a ci gaba da sauraron ƙarar ɗan China, amma hakan ba ta yuwu ba sakamakon zaman sauraron kararrakin zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: NSA Na Shugaba Tinubu Ya Sa Labule Da Gwamnoni 5 a Abuja, Sahihan Bayanai Sun Fito

Me ya haɗa ƙarar da zabe da ta kisan Ummita?

An tattaro cewa alkalin da ke sauraron shari'ar kisan Ummita, mai shari'a Sunusi Ado Ma’aji, yana ɗaya daga cikin alƙalan da ke sauraron korafe-korafen babɓan zaɓen 2023 a wata jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan baku manta ba, lokacin da aka kashe marigayya Ummita da kuma labaran alaƙarta da ɗan China ya ja hankali tare da cece kuce a tsakanin mutane a Kano da sauran jihohin ƙasar nan.

Da farko ɗan China ya musanta halaka Ummita, wanda ake zargin ya daɓa mata wuƙa har lahira a cikin gidansu, amma daga bisani ya amsa laifin kisan.

An yi ta yaɗa cewa Frank Geng Quanrong ya kashe wa marigayyar kuɗi masu yawa a lokacin da suka shafe suna soyayya.

Amma a jawabin da ya yi a gaban Kotu, Ɗan China da ake zargi ya yi ikirarin cewa ya kashe wa Ummita zunzurutun kuɗi kusan miliyan N60m.

Kara karanta wannan

Da Dum-Dumi: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Manyan Alkalai 2 a Najeriya Suka Kwanta Dama

Kotun Zabe Zata Yanke Hukunci Kan Sahihancin Zaben Tinubu a 2023

Kuna da labarin Kotun sauraron karar zaben shugaban ƙasa ta fara shirye-shiryen yanke hukunci kan zaben da shugaba Tinubu ya lashe a 2023.

A zaman ranar Talata, Kotun ta aje hukunci kan karar da Atiku ya shigar, ta ce zata sanar da ranar yanke hukunci nan ba da jima wa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262