Mun Tara Sama da Tiriliyan N1tr Daga Cire Tallafin Man Fetur, Shugaba Tinubu

Mun Tara Sama da Tiriliyan N1tr Daga Cire Tallafin Man Fetur, Shugaba Tinubu

  • Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta tara maƙudan kuɗi da suka kai naira tiriliyan ɗaya daga cire tallafin man fetur a wata 2 da suka wuce
  • A jawabinn kai tsaye da ya gudanar ranar Litinin, shugaba Tinubu ya ce wasu 'yan tsirarin mutane ne suke kwashe kuɗin da sunan tallafi
  • Bola Tinubu ya kuma gargaɗi shugabannin jami'o'i, kwalejin fasaha da kwalejojin ilimi su guji kara kuɗin makaranta

FCT Abuja - Ya zuwa yanzu dai gwamnatin tarayya ta tattala sama da Naira Tiriliyan 1, biyo bayan cire tallafin man Premium Motor Spirit (PMS) wanda aka fi sani da man fetur a Najeriya.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana hakan cikin jawabin kai tsaye da ya yi wa 'yan Najeriya kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu Ya Sanar da Sabuwar Garaɓasa Ga Ɗaliban Najeriya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Mun Tara Sama da Tiriliyan N1tr Daga Cire Tallafin Man Fetur, Shugaba Tinubu Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaba Tinubu na cewa:

"A 'yan watanni biyu da muka yi a kan mulki, mun ceto zunzurutun kuɗi sama da naira tiriliyan ɗaya da ake warewa da sunan kuɗin tallafin fetur, wasu yan fasa kwauri da 'yan damfara suna wawushe su."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yanzu za mu yi amfani da wannan kudin ta yadda zaku amfana kai tsaye da ku da iyalanku."

Shugaban kasar ya kuma gargaɗi shugabannin jami'o'in Najeriya su shiga taitayinwu kan yawaitar ƙarin kuɗin makaranta na gaira ba dalili, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

A raba wa talakawa hatsi su rage zagi - Shugaba Tinubu

"Bugu da ƙari, shugaba Tinubu ya amince FG ta fitar da tan 200,000 na hatsi daga rumbunan ajiyarta domin tallafa wa talaka wa masara galihu a jihohi 36 da birnin tarayya Abuja."

Kara karanta wannan

Karin Albashi, Kayan Abinci, Motocin Gas Da Albishir 6 Da Bola Tinubu Ya Yi Yau

"Haka nan gwamnati na aiki ba ji ba gani domin tabbatar da cewa ɗalibai masu rauni suma za su iya cin gajiyar tsabar kudin kuɗin da kuma rarraba abinci."

- Inji Bola Ahmed Tinubu, shugaban Najeriya.

Shugaba Tinubu Ya Sanar da Sabuwar Garaɓasa Ga Ɗaliban Najeriya

A wani labarin na daban kuma Shugagan kasa Bola Ahmed Tinubu ya aminta da raba wa manyan makarantun gaba da sakandire motocin zirga-zirgar ɗalibai.

Matakin na ɗaya daga cikin kudirorin shugbaan ƙasa na ganin ɗalibai suna kai kawo a makarantunsu ba tare da shan wahala ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262