Manyan Alkalai 2 Na Najeriya Sun Kwanta Dama a Rana Daya

Manyan Alkalai 2 Na Najeriya Sun Kwanta Dama a Rana Daya

  • Shahararren alƙalin kotun ƙoli, mai shari'a Chima Centus Nweze, ya yi bankwana da duniya yana da shekara 64
  • A cewar rahotanni, mai shari'a Nweze ɗan asalin Obollo a ƙaramar Udenu ta jihar Enugu, ya mutu ne a ranar Lahadi 30 ga watan Yuli
  • Haka kuma, wani alƙalin babbar kotun tarayya, Peter Mallong ya riga mu gidan gaskiya a ranar Lahadi, 30 ga watan Yuli

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Enugu - Mai shari'a Chima Nweze na kotun ƙolin Najeriya ya koma ga mahaliccinsa.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, duk da cewa iyalansa basu fitar da sanarwa ba kan mutuwarsa, wani majiya ya bayyana cewa alƙalin ya mutu ne a ranar Lahadi, 30 ga watan Yulin 2023.

Mai shari'a Nweze ya kwanta dama
Nweze ya kwanta dama yana da shekara 64 Hoto: Sunny Myke, Ifeanyieze Jaachike Bobby
Asali: Facebook

Mai Shari'a Chima Nweze ya yi bankwana da duniya ne yana da shekara 64.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Hana Ministan Da Tinubu Ya Zabo Daga Rike Mukami? Lauya Ya Bayyana Gaskiya

Mai shari'a Nweze, wanda yake haifaffen Obollo, cikin ƙaramar hukumar Udenu ta jihar Enugu, an haife shi ne a ranar 25 ga watan Satumban 1958.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Marigayi Nweze yana daga cikin alƙalan da suka hana jam'iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) da Atiku Abubakar buƙatarsu ta duba manhajar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), lokacin da su ke ƙalubalantar nasarar zaɓen Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2019.

Haka kuma, Nweze yana daga cikin alƙalan da suka yanke hukuncin kotun ƙoli wanda ya tabbatar da shugaban majalisar dattawa na wancan lokacin, Sanata Ahmed Lawan, a matsayin ɗan takarar jam'iyyar APC na kujerar Sanatan Yobe ta Arewa, a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.

Alƙalin babbar kotun tarayya ya riga mu gidan gaskiya

Rajistaran babbar kotun tarayya, Hassan Amida Sulaiman, ya sanar da mutuwar mai shari'a Mallong a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin da safe, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Emefiele: Peter Obi Ya Dau Zafi Kan Takaddamar Jami'an DSS Da Na Gidan Yari a Kotu, Ya Bayyana Matakin Da Ya Dace a Dauka

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Cikin baƙin ciki na ke sanar da mutuwar mai shari'a Peter Mallong, alƙalin babbar kotun tarayya, wanda ya mutu a ranar Lahadi bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya a birnin tarayya Abuja.

Mai shari'a Peter Mallong, wanda ya fito daga jihar Plateau, an haife shi ne ranar 21 ga watan Janairun 1963 a garin Yauri dake jihar Kebbi.

Tsohon Kakakin Rundunar 'Yan Sanda Ya Kwanta Dama

A wani labarin kuma, tsohon kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya kums tsohon kwamishina ya riga mu gidan gaskiya.

Frank Odita ya yi bankwana da duniya yana da shekara 84 bayan ya yi fama da ƴar gajeruwar rashin lafiiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel