Halin Bera Ya Yi Yawa a Majalisa, an Tsiri Sace Wayoyin Sanatoci a Harabar Majalisar Dokoki
- Shugaban majalisar dattawa ya koka kan yadda ake yawan sata a harabar majalisar dokokin Najeriya a wannan karon
- An yiwa sanatoci da yawa satan wayoyinsu a harabar majalisa baya ga yadda aka addabe su da yawan bara a harabar
- Ya zuwa yanzu, ana gyaran ginin majalisar dokokin Najeriya bayan da ya lalace saboda jimawan da ya yi
FCT, Abuja – Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawa ya koka kan yadda ‘yan baranda ke yawan shiga harabar majalisa tare da sace wayoyin sanatoci.
Ya bayyana cewa, ana samun mutane da basu cancanta da shiga harabar ba su na shiga suna barnar illata sanatocin kasar.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin ganawa da wata tawagar ma’aikatan majalisar da suka kai masa ziyarar ban girma, Vanguard ta ruwaito.
Yadda aka addabi sanatoci da sata a harabar majalisa
Ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Muna sane da cewa ana gyara ginin gaba dayansa. Dole ne mu kuma kula da muhallin. Ba wai batu ne ma'aikata ba, za mu so mu ga harabar da tsabta da aminci.
"Sanatoci da yawa sun rasa wayoyinsu saboda kwararowar mutane cikin ginin."
Sanatoci na cikin zaman dar-dar a majalisa
Shugaban majalisar dattawan ya jaddada cewa ‘yan majalisar na cikin barazana saboda kasancewar ‘yan baranda da yawa shiga harabar majalisar, Opinion Nigeria ta tattaro.
A cewar Akpabio, yayin da NASS ta 10 ta zauna don ayyukan majalisa, ’yan baranda da mutanen da ba su da wata alaka da harabar, sun yi ca a cikinta.
Akwai alamar aukuwar rashin tsaro a majalisa
A bayanansa, ya ce mutane suna shiga suna, suna bara tare da haifar da alamun rashin tsaro ga ‘yan majalisa da ma’aikatan majalisar dokokin kasar.
A tun farko, an fara gyaran majalisar dokokin Najeriya biyo bayan yadda ginin ya lalace sakamakon jimawa da ya yi.
Akpabio ya ce gwamnatin Tinubu za ta kara albashin ma’akatan Najeriya
A wani labarin, shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu za ta kara albashin ma’aikata domin rage musu radadin da cire tallafin man fetur ya jefa su a ciki.
Ya bayyana hakan ne a yayin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji, da tawagarsa a ofishinsa da ke Abuja ranar Talata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Shugaban na Majalisar Dattawa, ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya na sane da irin wahalhalun da ‘yan kasa ke sha sakamakon cire tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng