Kungiyar ECOWAS Ta Ba Sojoji NIjar Wa'adin Kwana Bakwai Su Mayar Da Bazoum Kan Kujerarsa

Kungiyar ECOWAS Ta Ba Sojoji NIjar Wa'adin Kwana Bakwai Su Mayar Da Bazoum Kan Kujerarsa

  • Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) ta sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar wa'adin kwana bakwai
  • Ƙungiyar ta ba sojojin wa'adin kwana bakwai su saki Shugaba Bazoum tare da mayar da shi kan muƙaminsa na shugaban ƙasa
  • Ƙungiyar ta nuna shirinta na amfani da ƙarfin soja wajen dawo da doka da oda a Nijar idan sojojin suka bijire

FCT, Abuja - Ƙungiyar raya tattalin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) ta bayar da wa'adin kwanaki bakwai ga sojojin da suka kifar da mulki a Jamhuriyar Nijar da su mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan kujerarsa ko su fuskanci takunkumi kala-kala.

Ƙungiyar ta kuma umarci manyan hafsoshin tsaro na ƙasashenta da su tattauna cikin gaggawa kan yadda za su samar da hanyoyin yin amfani da ƙarfin soja domin dawo da doka da oda a ƙasar, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnan Jihar Arewa Ya Sanya Dokar Kulle a Jiharsa, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

ECOWAS ta ba sojojin Nijar wa'adin kwanaki 7
ECOWAS za ta yi amfani da karfin soja kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar Hoto: @Channelstv
Asali: Twitter

Ƙungiyar ECOWAS, wacce ta ɗauki Bazoum a matsayin halastaccen shugaban ƙasar, ta yi barazanar kulle iyakoki da hana jirage yawo a sararin samaniyar Nijar, idan har sojojin basu yi abinda tace ba a cikin wa'adin da ta basu.

Wannan dai shi ne matsayar da aka cimmawa a taron shugabannin ƙasashe da gwamnatin ECOWAS, wanda aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock Villa a birnin tarayya Abuja, ranar Lahadi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sharuɗɗan da ƙungiyar ECOWAS ta Gindaya

ƙungiyar ECOWS ta yi kiran da a gaggauta sakin Shugaba Bazoum tare da mayar da shi kan muƙaminsa na shugabancin Jamhuriyar Nijar, da dawo da amfani da kundin tsarin mulki a ƙasar.

Yin fatali da murabus ɗin da ka iya fitowa daga ɓangaren Bazoum, haramcin ci gaba da tsare Bazoum tare da ɗora alhakin kula da lafiyarsa da ta iyalansa da jami'an gwamnatinsa akan wuyan sojojin da suka yi juyin mulkin.

Kara karanta wannan

Janar Tchiani: Muhimman Abubuwan Sani Guda 5 Dangane Da Sojan Da Ya Kitsa Hambarar Da Gwamnati a Jamhuriyar Nijar

Idan har sharuɗɗan da ƙungiyar ta gindaya ba a cika su ba cikin sati ɗaya, ƙungiyar za ta ɗauki matakan da suka dace domin dawo aiki da kundin tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar, cewar rahoton Channels tv.

Matakan da ECOWAS ta ɗauka

Dakatar da dukkanin hada-hadar kasuwanci tsakanin ƙasashen ECOWAS da Nijar.

Kulle dukkanin asusun ajiya na Jamhuriyar Nijar a babban bankin Aqua da kulle dukkannin kuɗaɗen Nijar da na ma'aikatunta dake a bankunan kasuwanci.

Dakatar da bayar da dukkanin wani tallafin kuɗi na hanyoyin haɗa-haɗar kuɗaɗe musamman EBID.

Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Kan Juyin Mulkin Nijar

Rahoto ya zo cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi martani kan juyin mulkim da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar.

Shugaba Tinubu wanda shi ne shugaban ƙungiyar ECOWAS ya bayyana cewa ko kaɗan ƙungiyar ba za ta lamunci juyin mulkin da aka yi a Nijar ba.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga da Yaransa 4 da Suka Addabi Mutane a Jihohin Arewa 2

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng