Da Dumi-Dumi: Gwamnan jihar Adamawa Ya Sanya Dokar Ta Baci a Jihar
- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya sanya dokar kulle ta tsawon sa'o'i 24 a gaba ɗaya ƙananan hukumonin jihar 21
- Gwamnan ya buƙaci al'ummar jihar da su bi umarnin sanya dokar kullen ta tsawon sa'o'i 24 domin kare lafiyarsu
- Finitiri ya yi bayanin cewa an yanke shawarar sanya dokar kullen ne bisa ƙaruwar rikicin ƴan daba da su ke farmakar mutane da wuraren kasuwanci
Yola, jihar Adamawa - Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya sanar da sanya dokar ta ɓaci a dukkanin ƙananan hukumomin jihar 21, tun daga ranar Lahadi, 30 ga watan Yulin 2023.
A cikin wata ƴar gajeruwar sanarwa da gwamnan ya fitar a shafinsa na Twitter, @GovernorAUF, Fintiri ya bayyana cewa an sanya dokar ta ɓacin ne saboda ƙaruwar rikice-rikicen ƴan daba da suke farmakar mutane da wajen kasuwancinsu.
Emefiele: Peter Obi Ya Dau Zafi Kan Takaddamar Jami'an DSS Da Na Gidan Yari a Kotu, Ya Bayyana Matakin Da Ya Dace a Dauka
Gwamnan ya ƙara da cewa mutanen da su ke ayyuka na musamman masu halastaccen katin shaidar aiki kaɗai za a ba iznin yin zirga-zirga.
Tsawon lokacin da za kasance a kulle
Gwamna Fintiri ya buƙaci al'ummar jihar da su bi umarnin dokar ta ɓacin ta tsawon sa'o'i 24.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanarwar na cewa:
"Daga ranar Lahadi, 30 ga watan Yuli, ni gwamna Ahmadu Umaru Fintirina na sanya dokar ta ɓaci ta sa'o'i 24 saboda ƙaruwar rikicin ƴan daba dake farmakar mutane da wuraren kasuwanci."
"An haramta zirga-zirga face ga masu ayyuka na musamman da su ke da halastaccen katin shaidai aiki. Kare lafiyarku shi ne abu mafi muhimmanci a wajen mu, ku daure ku bi wannan umarnin domin amfanin kowa."
Gwamna Fintiri Ya Gatanta Ma'aikata Da 'Yan Fansho a Adamawa
A wani labarin kuma gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya shirya ragewa ma'aikata da ƴan fansho a jihar Adamawa raɗaɗin da su ke sha a dalilin cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi.
Gwamnan ya amince da bayar da tallafin N10,000 duk wata ga ma'aikata da ƴan fansho a jihar. Tallafin dai za a bayar da shi ne har na tsawon wata shida domin rage ɗaɗaɗin da ake ciki.
Asali: Legit.ng