Kotu Ta Umarci Tsohon Gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa Ya Yi Bayanin Yadda Ya Kashe N200bn

Kotu Ta Umarci Tsohon Gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa Ya Yi Bayanin Yadda Ya Kashe N200bn

  • Wata babbar kotun tarayya ta bayar umarnin yin bayani kan yadda tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya kashe N200bn
  • Kuɗaɗen dai an karɓo su ne daga hukumar ilmin bai ɗaya ta ƙasa da asusun gwamnatin tarayya domin bunƙasa ilmi a jihar
  • Kotun tana son a yi mata cikakken bayani kan yadda aka kashe kuɗaɗen da ayyukan da aka gudanar da kuɗaden

Jihar Legas - Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin Legas, ta bayar da umarnin yin cikakken bayani kan yadda gwamnatin tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ta kashe N200bn kuɗin ilmi a jihar, rahoton PM News ya tabbatar.

Gwamnatin ta Okowa ta amso kuɗaden ne daga hukumar ilmin bai ɗaya ta ƙasa (UBEC) da asusun gwamnatin tarayya.

Kotu ta umarci Okowa ya yi bayanin yadda ya kashe N200bn
Kotu na son Okowa ya yi bayanin yadda ya kashe N200bn Hoto: @IAOkowa
Asali: Twitter

Kotun ta umarci gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori da ya bayyana daki da daki na yadda gwamnatin Okowa ta kashe kuɗin daga shekarar 2015 zuwa 2019, ciki har da ayyukan da aka yi domin ciyar da ilmin firamare gaba a jihar da wuraren da aka yi ayyukan.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Wakilan Ƙungiyar Kwadugo NLC Sun Fice Daga Fadar Shugaban Kasa, Bayanai Sun Fito

Mai shari'a Daniel Osiagor ya yanke wannan hukuncin ne a ƙara mai lamba FHC/L/CS/803/2019, wacce ƙungiyar SERAP ta shigar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Justice Osiagor ya umarci gwamnatin jihar Delta ta yi bayanin yadda gwamnatin Okowa ta kashe sama da N7.28bn da ta karɓa daga wajen hukumar UBEC daga shekarar 2015 zuwa 2017, da N213bn da ta karɓa daga wajen asusun raba dai-dai na gwamnatin tarayya a shekarar 2018, akan N17.8bn kowane wata.

Ƙarar SERAP na zuwa ne bayan wata yarinya ƴar shekara bakwai mai suna Success Adegor, an koro ta gida saboda iyayenta sun kasa biyan haramtattun kuɗin makaranta na N900 da kuma taɓarɓarewar makarantar da take karatu ta 'Okotie-Eboh Primary School 1.'

Justice Osiagor ya umarci gwamnatin ta yi bayanin makarantun firamaren da suka amfana da ayyukan da aka gudanar domin samar da ilmin firamare kyauta a jihar Delta, da bayani kan kuɗin makaranta da kuɗin littatafai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel