“Mahaifiyarmu Ita Ce Jarumarmu”: Kyawawan Yan Mata Uku Yan Ciki Daya Sun Zama Matukan Jirgin Sama

“Mahaifiyarmu Ita Ce Jarumarmu”: Kyawawan Yan Mata Uku Yan Ciki Daya Sun Zama Matukan Jirgin Sama

  • Wasu yan mata uku da suka fito ciki daya sun zama matukan jirgin kasa, kuma an gano su a wani hoto da ya yadu a Twitter
  • Yan matan, Mopelola Makinde, Oluwaseun Makinde, da Oluwafunmilayo Makinde, sun fito ne daga jihar Ondo, kuma mahaifinsu ma matukin jirgin sama ne
  • Mopelola, Oluwaseun da Oluwafunmilayo sun fito kasance cikin yara mata bakwai da mahaifiyarsu ta haifa

Wasu yan mata yan Najeriya uku da suka fito daga jihar Ondo wadanda iyayensu daya sun zama matukan jirgin sama.

Wani mai amfani da Twitter Oluyemi Fasipe ne ya wallafa hoton yan matan kuma tuni ya yadu tare da haifar da martani masu dadi daga bangarori daban-daban.

Yan gida daya su uku sun zama matukan jirgin sama
“Mahaifiyarmu Ita Ce Jarumarmu”: Kyawawan Yan Mata Uku Yan Ciki Daya Sun Zama Matukan Jirgin Sama Hoto: @YemieFash and Women of Power Africa.
Asali: Twitter

Yan uwan junan sun sanya kayansu na tukin jirgi yayin da suka tsaya tare domin daukar hoto wanda ya dauka hankalin mutane.

Kara karanta wannan

“Ban Taba Haduwa Da Mahaifina Ko Sau 1 Ba”: Ɗan Najeriya Da Ya Shafe Shekaru 29 Yana Nema Danginsa

Yan gida daya 3 daga jihar Ondo sun zama matukan jirgin sama

Sunayen yan uwan junan sune; Mopelola Makinde, Oluwaseun Makinde, da Oluwafunmilayo Makinde.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abun da zai kara baka sha'awa da wadannan yan mata shine sun kasance daga cikin 'ya'ya mata bakwai da mahaifiyarsu ta haifa.

Wani karin abun mamaki game da su shine cewa mahaifinsu, Kyaftin Wale Makinde, shima matukin jirgin sama ne kuma ya yi aiki da hukumar jirgin sama na Najeriuya, NCAA.emerges/'

Yayin da yake wallafa hoton, Fasipe ya rubuta:

"Mopelola da Oluwaseun Matukan Jirgi mai saukar ungfulu ne, yayin da Oluwafunmilayo ta kasance matukiyar Jirgin Sama ce. 'Yan'uwa mata 3 suna tashi kuma suna zaune cikin farin ciki a gidan aurensu."

Mahaifiyarmu ce gwanar mu

Ruutun ya ja hankalin daya daga cikin yan matan, @fummzzy, ta rubuta cewa mahaifiyarsu ce jarumar labarin.

Kara karanta wannan

Kace-Nace Yayin Da 'Yan Najeriya Suka Soki Yadda Tinubu Ya Zabi Ministoci, Sun Bayyana Abin Da Ya Kamata

"Ita ce Komai! A cikin al'ummar da mace ke da 'yan mata a matsayin yara. 'yan mata bakwai a takaice."

Jama'a sun yi martani

@kolamaks ta yi martani:

"Na sani!! Wannan shine aikin da nake mafarkin yi. Na tsinci kaina a ahlin Makinde da bai dace ba."

@adewryght ya yi martani:

"Ya kamata wannan ya shiga kundin bajinta na Guiness ace iyali hudu matukan jirgin sama. Uba da yaransa mata uku."

Bidiyon matasa da ke takowa daga Kmaru don karatu a Najeriya ya tsuma zukata

A wani labari na daban, mun ji cewa wani bidiyo na wasu yan makaranta daga Kamaru wadanda ke tafiya a kafa zuwa Najeriya ya tsuma zukatan mutane da dama.

A kokarinsu na samun ilimi mai inganci, yaran wadanda ke zama a wani kauye a Kamaru suna tafiya a kafa har Najeriya don zuwa makaranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng