Matashi Ya Bude Sana’ar Siyar Da Keke Yayin da Farashin Man Fetur Ya Haura Sama a Najeriya

Matashi Ya Bude Sana’ar Siyar Da Keke Yayin da Farashin Man Fetur Ya Haura Sama a Najeriya

  • Yayin da farashin man fetur ke ci gaba da tashin gwauron zabi a Najeriya, wani dan kasuwa ya fara sana'ar siyar da keke
  • Mutumin mai suna Morris Monye ya ce kekunansa sun iso kasar kwanan nan kuma yana siyar da wasu kan 400k, wasu kuma a kan N350k
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da yan Najeriya da dama ke neman hanyoyi na daban da za su dunga sufurin kansu yayin da man fetur ya haura sama

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani hazikin dan kasuwa a Najeriya ya shigo da kekuna cikin kasar domin siyar da su yayin da farashin man fetur ya haura sama sosai.

Mutumin mai suna Morris Monye ya wallafa bidiyoyin kekunan a Twitter sannan ya ja hankalin mutane masu neman wasu hanyoyin sufuri.

Kekunan siyarwa da wani dan kasuwa ya shigo da su Najeriya saboda tsadar fetur
Matashi Ya Bude Sana’ar Siyar Da Keke Yayin da Farashin Man Fetur Ya Haura Sama a Najeriya Hoto: @Morris_Monye.
Source: Twitter

Monye ya ce bai dade ba da kekunan suka shigo Najeriya sannan cewa yana tallata su domin ra'ayin kwastamomi da za su so fara amfani da kekuna don rage tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

“Aikin Nan Akwai Hatsari Sosai”: Mai POS Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Karbi Jabun N100K Daga Kwastoma, Bidiyon Ya Yadu

Wani mutum ya fara siyar da kekuna yayin da farashin man fetur ya haura a Najeriya

Ya ce kekunan iri biyu ne. Yayin da ake siyar da daya kan N400k, wasu na nan a kan N350k kowani daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ake siyarwa N400k yana da cikakken wuta, hular kwano, makulli da sauransu.

Da yake wallafa hotunan a Twitter, Monye ya rubuta:

"Kekuna 50 sun iso. Hoton farko N400k (karafuna na musamman, cikakken wuta, hular kwano, makulli da sauransu). Hoto na biyu 350k ne. Za a iya kai maka duk inda kake a Najeriya."

Yayin da farashin man fetur ya haura zuwa N600 a wasu yankunan Najeriya, mutane da dama na neman hanyoyin zirga-zirga kamar su kekuna.

Kalli hotunan a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Yusuf24626106 ya ce:

"Ina ma ace zan iya siyan wannan. Amma da izinin Allah, zan siya haajarka kwanan nan."

@kaurday ta yi martani:

"Yan Najeriya na iya yanke shawarar komawa ga satar kekuna kamar yadda suke yi a UK a yanzu."

Kara karanta wannan

“Ban Taba Haduwa Da Mahaifina Ko Sau 1 Ba”: Ɗan Najeriya Da Ya Shafe Shekaru 29 Yana Nema Danginsa

Matashi ya koka bayan ya mayar da motarsa zuwa mai amfani da gas

A wani labarin, mun ji cewa dandalin soshiyal midiya ya dauki dumi bayan an wallafa bidiyon wata mota da ta dungi daukar zafi a babban titi a TikTok.

A cewar @user145586464 a TikTok, motar ta fara daukar zafi ba kakkautawa a kan babban titin bayan an mayar da ita zuwa mai amfani da iskar gas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng