Gobara Ta Lakume Kadarorin Miliyoyin Naira a Jihar Kwara
- Wata mummunar gobara ta auku a rukunin wasu shagunan kasuwanci a birnin Ilorin na jihar Kwara
- Gobarar ta tashi ne a dalilim wutar lantarki inda ta laƙume kadarori na miliyoyin naira a rukunin shagunan kasuwancin
- Jami'an hukumar kashe gobara ta jihar sun samu nasarar daƙile gobarar ba ta kai ga sauran shagunan ba inda ta tsaya akan shago ɗaya kawai
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kwara - A ranar Asabar hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta kubutar da kadarorin da sun kai na N148.7m, lokacin da gobara ta kama rukunin wasu shaguna 20 a birnin Ilorin.
Gobarar wacce ta auku a dalilin tartsatsin wutar lantarki, ta laƙume kadara wacce ta fi ta N3.2m.
A cewar kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle, gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 05:57 na safiyar ranar Asabar, 29 ga watan Yulin 2023, cewar rahoton Nigerian Trbune.
A kalamansa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Gobarar ta auku ne akan layin Fufu, unguwar Sabo-Oke a cikin birnin Ilorin, ƙaramar hukumar Ilorin ta Gabas a jihar Kwara
"Bayan mun samu kiran gaggawa daga wajen wani mai suna Mr Thomas, nan da nan muka aike da jami'an mu zuwa wajen da gobarar ta auku."
Hassan Adekunle ya ci gaba da cewa bayan jami'an sun isa wajen, sun hanzarta wajen daƙile gobarar cikin gaggawa domin hanata ci gaba da yaɗuwa zuwa ga sauran shagunan, rahoton Daily Post ya tabbatar.
An ceto kadarorin miliyoyin naira daga salwanta
Ya bayyana cewa gobarar ta ritsa da shago ɗaya cikin shaguna 20 na wajen rukunin wasu gine-gine, inda aka samu nasarar daƙile asarar miliyoyin naira da gobarar ta so haddasa wa.
"A saboda haka, darektan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Prince Falade John Olumuyiwa, yana kira ga jama'a da su riƙa kashe kayan lantarkinsu kafin su kwanta barci domin hakan zai rage aukuwar gobara a gidaje, ofisoshi da shaguna." A cewarsa.
Gobara Ta Lakume Shaguna a Kano
A wani labarin kuma, wata mummunar gobara ta laƙume wasu shaguna a kasuwar Rimi dake a cikin birnin Kano.
Gobarar wacce ta auku a cikin dare, ta tashi ne a dalilin tartsatsin wutar lantarki ta laƙume shaguna 10 a cikin Kasuwar ta Rimi.
Asali: Legit.ng