Bidiyon Yara Da Ke Tafiya a Kafa Daga Kamaru Zuwa Najeriya Don Samun Ilimi Ya Tsuma Zukata
- Wani dan Najeriya ya nemi taimako a madadin wasu kananan yara da ke tafiya a kafa zuwa makaranta duk kwanan duniya
- A cewar mutumin, yaran na tafiya daga Kamaru zuwa Najeriya sannan su koma Kamaru duk a kafa
- Masu amfani da soshiyal midiya da dama sun yi martani ga bidiyon inda wasu da dama suka nuna sha'awar son taimaka masu
Wani bidiyo na wasu yan makaranta daga Kamaru wadanda ke tafiya a kafa zuwa Najeriya ya tsuma zukatan mutane da dama.
A kokarinsu na samun ilimi mai inganci, yaran wadanda ke zama a wani kauye a Kamaru suna tafiya a kafa har Najeriya don zuwa makaranta.
Wani bawan Allah ya ga yaran suna tattaki don komawa Kamaru sannan ya tsayar da su ya yi masu tambayoyi kan halin da suke ciki.
Yaran sun bayyana cewa basu da kudin hawa babur kuma idan ma sun biya babur, ba zai kai kauyensu a domin babu hanyoyi masu kyau a kauyensu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar yaran, babu makaranta da ke budewa a Kamaru saboda rikicin da ke gudana a chan.
Bawan Allan ya kira masu babur biyu sannan ya biya su N20k domin su dunga kai yaran boda sannan daga chan, za su taka zuwa kauyensu tunda babu abun hawan da zai kai su chan.
Jama'a sun yi martani
@237johnscott2 ya ce:
"Abu guda da nake yawan fadi shine yan Najeriya sun fi kowa kirki a Afrika duk da tsanar da duniya baki daya ta yi masu. Karin soyayya daga Kamaru."
@ay_komo ta bayyana:
"Na taba irin tafiya haka zuwa makaranta. Allah ya albarkaceka yallabai. Idan suna bukatar iyayen goyo a sanar da ni. Da kuma dama garesu na zuwa karatu a Kanada. don Allah."
@tebitcindybright ta ce:
"Allah ya yi maka albarka yallabai mu yan Kamaru muna godiya gareka sosai yallabai Allah ya daukaka ka."
@godsfavorite398 ta yi martani:
"Yan Najeriya na da kirki wallahi dalilin da yasa nake son ku kenan mungode yallabai da wannan karamci Allah ya albarkace ka."
Kalli bidiyon a kasa:
Ma'aikacin banki ya wawure kudi daga asusun kwastoma da katin ATM dinta
A wani labari na daban, wani tsohon ma'aikacin banki, Uchenna Emmanuel, ya bayyana yadda ya yi kuskuren amfani da katin ATM din kwastoma wajen cire kudi sau biyar.
Tsohon ma'aikacin bankin na daya daga cikin bankunan zamani ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 28 ga watan Yuli, 2023, yayin da rundunar yan sandan Ondo ta gurfanar da shi a Akure.
Asali: Legit.ng