Bokan Da Aka Sace a Anambra Ya Magantu Bayan Ya Shaki Iskar 'Yanci
- Shahararren bokan nan na jihar Anambra da ya shaƙi iskar ƴanci bayan binduga sun ƙwamushe shi ya magantu
- Chukwudozie Nwangwu ya bayyana cewa gudun kada a rasa rayuka ne ya sanya ya yarda ƴan bindiga suka sace
- Bokan dai ya shaƙi iskar ƴanci ne bayan ya kwashe kwanaki shida a hannun masu garkuwa da mutanen da suka sace shi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Anambra - Shahararren bokan nan na jihar Anambra, Chukwudozie Nwangwu, wanda ƴan bindiga suka sace a ranar Lahadin da ta gabata, ya shaƙi iskar ƴanci.
Nwangwu ya shaƙi iskar ƴanci ne bayan ya kwashe kwana shida a hannun masu garkuwa da mutanen da suka yi awon gaba da shi, cewar rahoton Premium Times.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an sako bokan ne da safiyar ranar Asabar, bayan an biya kuɗin fansa masu yawa waɗanda ba a bayyana ko nawa ba ne.
Nwangwu a safiyar ranar Asabar, ya tabbatar da sako shi da aka yi a wani bidiyo wanda ya yaɗu a manhajar Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon an nuna bokan yana gayawa magoya bayansa yadda miyagun suka kawo masa farmaki.
Ya bayyana cewa yana cikin ɗaya daga cikin otel ɗinsa da misalin ƙarfe 11:30 na dare a ranar lokacin da wani mai suna Okey Japan, ya buƙace shi da ya zo wani otel ɗin.
A kalamansa:
“Okey Japan ya bayyana cewa yana son ganina saboda wannan ne karon farko da ya je otel ɗina. Sai na tafi a motata zuwa otel ɗin ba tare da kowa ba. Ko minti 30 ban yi da zuwa ba a ka fara harbe-harben bindiga."
Dalilin da ya sanya na yarda suka tafi da ni - Chukwudozie
Bokan ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun halaka masu tsaron lafiyarsa mutum biyu da wasu mutane daban a harabar otel ɗin.
"Lokacin da na fito domin na ga abinda ke faruwa, sai suka fara harbi na, amma nasan ko waye ni. Daga ƙarshe sai suka cusa ni cikin motarsu suka tafi da ni." A cewarsa.
"Idan da ina son na gudu, da na gudu, amma na ga mutanen da za su harba idan na gudu. Abinda na yi, na yi shi ne domin na ceto rayuwar sauran mutanen. Na bi su ne saboda kada ayi zargin cewa ni ne na kawo masu garkuwa da mutanen."
Bokan ya bayyana cewa ran shi ya ɓaci kan 'shirmen' bayanin da wasu mutane ke yi a gidajen rediyo da soshiyal bayan an sace shi.
Bai bayyana inda aka tafi da shi ba da abinda ya faru a inda aka ajiye shi.
An Sako Babban Boka a Anambra
Da zu rahoto ya zo cewa shahararren bokan nan na jihar Anambra ya kuɓuta daga hannun miyagun da suka yi garkuwa da shi.
Chukwudozie Nwangwu ya kuɓuta ne na bayan ya kwashe kwanaki shida a hannun waɗanda suka sace shi.
Asali: Legit.ng