Mai POS Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Karbi Jabun N100K Daga Kwastoma, Bidiyon Ya Yadu

Mai POS Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Karbi Jabun N100K Daga Kwastoma, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata matashiya yar Najeriya ta koka sosai a soshiyal midiya bayan ta yi asarar makudan kudade a hannun yan damfara
  • A cewar matashiyar wacce ta karaya, wani dan damfara da ya ziyarci shagonta na POS ya biya ta da jabun kudi
  • Bayan ta bayyana halin da ta shiga, mutane da dama sun garzaya sashin sharhi domin tausaya mata a kan wannan babban asara da ta yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata mai sana'ar POS ta fashe da kuka bayan mummunan al'amari da ya ritsa da ita awajen aikinta.

A cewar matashiyar da zuciyarta ya karaya mai amfani da shafin @ faviebliz, wani dan damfara ya ziyarci shagonta a matsayin kwastoma ya bata jabun kudi naira 100,000.

Mai POS ta hadu da dan damfara a shagonta
Mai POS Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Karbi Jabun N100K Daga Kwastoma, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @faviebliz/TikTok.
Asali: TikTok

Ta saki wani bidiyo mai ban tausayi da kudaden sannan ta fashe da kuka a cikin bidiyon yayin da jama'a suka tausaya mata.

Kara karanta wannan

"Gara Fetur Sau Dubu": Wata Mata Ta Koka Bayan Gas 12kg Da Ta Zuba a Janaretonta Ya Kare Cikin Awanni 7

Martanin jama'a yayin da wani mutum ya damfari mai POS N100k

@tosinayanwole207 ta yi martani:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yi hakuri madam amma nan gaba ki fara karbar kudin sannan ki duba da kyau kafin ki tura kudin, Allah ya cike maki gurbin."

@dammie178 ta ce:

"Ki je bankinki yar uwa. Za su taimaka maki wajen gano mutumin. Bayan haka ai kina da gaba daya bayanansa da ya baki don tura kudin ko?"

@tosinayanwole207 ta rubuta:

"Ya zama dole mu zamo masu lura wannan sana'a tamu na da matukar hatsari kuma yanzu babu kudi a ciki kawai dai muna jurewa ne."

@archibong59 ya kara da cewa:

"Ki je banki, ki yi korafi za su toshe asusun daga yin kowani irin hada-hadar kudi, sannan idan ya je banki yin korafi. Za su fada masa dalili."

Kalli bidiyon a kasa:

Kara karanta wannan

Iyalin Da Kowa Mai Facin Tayoyi Ne Harda Uba, Uwa Da Dansu, Bidiyonsu a Bakin Aiki Ya Yadu

Dan Najeriya ya koka bayan ya mayar da motarsa mai amfani da gas

A wani labarin kuma, mun ji cewa dandalin soshiyal midiya ya dauki dumi bayan an wallafa bidiyon wata mota da ta dungi daukar zafi a babban titi a TikTok.

A cewar @user145586464 a TikTok, motar ta fara daukar zafi ba kakkautawa a kan babban titin bayan an mayar da ita zuwa mai amfani da iskar gas. Abun ya kai ga wuta ya tashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng