Wata Mata Ta Koka Bayan Gas 12kg Da Ta Zuba a Janaretonta Ya Kare Cikin Awanni 7
- Bidiyon wata mata tana korafi bayan ta yi amfani da gas a janaretonta ya yadu a soshiyal midiya
- Ta yi ikirarin cewa ta yi amfani da iskar gas 12kg wajen kunna janaretonta amma tsawon awanni bakwai kacal ya dauke ta
- Ta nuna gajiyawarta sannan ta bayyana cewa duk da tsadar man fetur, ya fi iskar gas sau dubu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Bidiyon ban dariya na wata mata da ya yadu a TikTok ya ja hankalin masu kallo da dama a soshiyal midiya.
A cikin bidiyon, matar ta bayyana halin da ta shiga bayan ta koma ga amfani da gas a madadin man fetur wajen gudanar da janaretonta.
Ta bayyana cewa ta siya iskar gas 12kg daga wani shago da ke kusa da ita sannan ta hada shi da janaretonta, tana ganin za ta samu rarar wasu yan kudade sannan ta mori wutarta ba tare da tangarda ba.
Wata mata ta nuna takaicinta bayan ta yi amfani da iskar gas 12kg cikin awanni 7
Sai dai kuma, abun takaici, ta gano cewa gas din ya kone kurmus cikin awanni bakwai da fara amfani da shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ta kadu matuka sannan abun ya bata mata rai sosai, inda take tunanin cewa duk da tsadar da man fetur ya yi, ya fi iskar gas sau dubu.
Ta nuna fushi da takaicinta a hanyoyi daban-daban, lamarin da ya sa mutane da dama dariya da kuma yin tsokaci kan halin da ta shiga.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Quam Omotosho ta yi martani::
"Ki koma ga Solar, Solar ya fi inganci hajiya."
user8111961888547 ya ce:
"mama akwai inda yake yoyo a hancin."
adesanya adeniyi sam ya ce:
"4kg na gas dina na yin awanni 14, a bangarena ya yi."
Matashi ya baje kolin janaretonsa nara amfani da fetur, da hasken rana yake aiki kuma baya kara
A wani labarin, Legit.ng ta kawo a baya cewa wani matashi dan Najeriya ya maje kolin wani janareto mai amfani da hasken rana da baya bukatar man fetur.
A wani bidiyon TikTok, ya yi amfani da janarfeton wajen kunna wasu kayan wuta sannan ya bayyana cewa yana da karfin 500-watt.
Asali: Legit.ng