Cire Tallafin Fetur: Shugabannin Kwadugo Sun Fice Daga Fadar Shugaban Kasa
- Wakilan ƙungiyar kwadugo ta ƙasa (NLC) sun fice daga fadar shugaban ƙasa ba tare da an yi taro ba ranar Jumu'a
- FG na ci gaba da kokarin rarrashin NLC da ƙawayenta bayan sun yi barazanar shiga yajin aiki ranar 2 ga watan Agusta
- Mambobin NLC sun zargi wakilan gwamnati da amfani waɗannan tarukan wajen yaudarar 'yan Najeriya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Ƙungiyar kwadago ta fice daga wurin taron da aka shirya da wakilan shugaban ƙasa a fadar Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja ranar Jumu'a.
Daily Trust ta tattaro cewa an shirya taron ne domin tattauna batun tallafin rage radaɗin da gwamnatin tarayya zata raba wa yan kasa bayan cire tallafin man fetur.
Joe Ajaero, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, ya jagoranci tawagarsa zuwa ofishin shugaban ma’aikata, inda taron zai gudana, amma ba da jimawa ba suka fito daga Villa.
A ranar Laraba da ta gabata, kwamiti na musamman ya fara zama da wakilan gwamnatin tarayya kuma suka cimma matsayar dawowa ranar Jumu'a domin jin ba'asi kan buƙatun NLC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
FG ce ta kafa kwamitin domin duba hanyoyin da ya dace a bi a rage radaɗin cire tallafin man fetur ga ma'aikata.
Amma taron bai yuwu ba saboda ƙaranci halartar mutane inji wani mamban kwamiti,.kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Wace matsala da jawo cikas a taron?
Kungiyar kwadagon ta zargi gwamnatin tarayya da yin amfani da tarurrukan a matsayin hujja wajen yaudarar ‘yan Najeriya.
Wata majiya a wajen taron ta tabbatar da cewa, ya kamata wasu kananan kwamitoci guda uku da suka hada da kwamitin sufuri, kwamitin gas da kuma kwamitin raba tsabar kudi su halarci taron.
A cewarsa, ana buƙatar waɗan nan kananan kwamitoci su hallara domin yi wa babban kwamitin bayanin matakan da aka dauka domin dakile illar tallafin man fetur ga ma'aikata.
Sai dai NLC ta yi ikirarin cewa jami'an gwamnati, waɗanda suka cika kananan kwamiticon, ba bu wanda aka gani ya zo wurin taron.
Wani daga cikin yan kwadugon ya ce:
“Ba su shirya taron ba, gaskiyar kenan. Wakilan gwamnati sun dage cewa ya kamata a ci gaba da taron duk da cewa ba a samu wata matsaya ba."
“Babu wanda muka haɗu da shi a wurin taron. Shugaban ma’aikatan ba ya nan, sun dauke mu tamkar wasu kananan yara ne.”
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Bai Wa Ministoci 28 Sabon Umarni, Sun Shiga Mataki Na Gaba
A wani labarin kuma Hadimin shugaban ƙasa, Sanata Abdullahi Gumel, ya ce sun fara tantance takardun waɗanda Bola Tinubu ya naɗa ministoci.
Gumel ya buƙaci dukkan waɗanda sunansu ya shiga jerin ministocin su je ofishinsa daga nan zuwa ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng