An Samu Ƙaruwar Masu Cutar 'Diphtheria' a Kano, An Kwantar Da Mutane 130 a Asibiti
- Aƙalla mutane 130 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar nan ta mashaƙo wato 'diptheria' a jihar Kano
- Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Yusuf ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai
- Ya alaƙanta yawaitar masu mashaƙon da ake samu da sakacin gwamantin da ta shuɗe wajen ƙin yin rigakafin cutar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ce ta ƙaddamar da cibiyoyin lafiya uku domin daƙile yaɗuwar cutar mashaƙo ta 'diptheria' da ake samu a jihar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu masu ɗauke da cutar har su 130 a faɗin jihar kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Gwamnatin Kano ta ɗauki duk matakan daƙile yaɗuwar cutar ta 'diptheria' a jihar
A yayin da yake jawabi ga manema labarai, kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Abubakar Yusuf, ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki duk matakan da suka dace wajen daƙile yaɗuwar cutar.
Aikin Likita, Banki Da Abubuwa 3 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Ministan Jonathan Da Ya Shiga Cikin Ministocin Tinubu
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya bayyana cewa sama da mutane 130 ne aka kwantar a asibiti a ranar Litinin ɗin da ta gabata sanadin cutar ta mashaƙo.
Yusuf ya ce bai kamata a ce jiha kamar Kano na fama da matsalar ta mashaƙo ba, inda ya alaƙanta yawaitar masu kamuwa da cutar da ake ƙara samu da rashin gudanar da rigakafi a gwamnatin baya da ta shuɗe.
Gwamna Abba Kabir ya ba da umarnin ɗaukar matakan da suka dace
Dakta Abubakar ya ce tuni gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta ba da umarnin ɗaukar duk matakan da suka dace wajen daƙile yaɗuwar cutar.
Ya bayyana cewa a yanzu haka an ware asibitoci guda uku da za su kasance mazaunin cibiyar da za a riƙa kula da waɗanda suka kamu da cutar kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Ya kuma shawarci ɗaukacin al'ummar jihar da su yi gaggawar zuwa asibiti a duk lokacin da suka ji alamomin cutar kamar yadda hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa (NCDC) ta ƙasa ta bayyana.
A farkon shekarar 2023 ne aka fara samun ɓullar cutar ta Diphtheria a jihar Kano, inda ta yi sanadin rasa rayuka da dama kafin a sami nasarar ɗaƙile ta.
Gwamnatin Kano ta soke lasisin 'yan Kannywood a jihar baki ɗaya
Legit.ng a baya ta kawo rahoton cewa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta sanar da soke lasisin 'yan masana'antar shirya finafinai ta Kannywood.
Shugaban hukumar tace finafinan Abba El-Mustapha ne ya sanar da hakan, inda ya ce sun ɗauki matakin ne domin tsaftace harkar fim a faɗin jihar.
Asali: Legit.ng