“Mahaifina Na Sane”: Budurwa Ta Bar Iyayenta Don Rayuwa Da Saurayi a Daji

“Mahaifina Na Sane”: Budurwa Ta Bar Iyayenta Don Rayuwa Da Saurayi a Daji

  • Wata yar Najeriya mai suna Mercy ta yi fice a soshiyal midiya bayan an gano ta a daji tare da saurayinta
  • Yayin da wasu mutane suka da suka ganta a dajin suka tunkareta, ta yi ikirarin cewa mahaifinta yana sane da inda take
  • A cewarta, iyayenta na fama da talauci sosai wanda shine dalilin da yasa dole ta koma zama da saurayinta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiyar yarinya mai suna Mercy daga cikin Delta ta haddasa cece0-kuce a TikTok bayan bidiyonta ya bayyana.

An gano yarinyar tana rayuwa a daji tare da saurayinta wanda ya fito daga jihar Akwa Ibom kuma yana aiki ne a wata gonar koko.

Matashiya ta koma zama da saurayinta a daji
“Mahaifina Na Sane”: Budurwa Ta Bar Iyayenta Don Rayuwa Da Saurayi a Daji Hoto: @whitesharkblob/TikTok.
Asali: TikTok

Da aka tambayeta kan dalilin da yasa ta baro gidansu don rayuwa a jeji, Mercy ta yi ikirarin cewa mahaifinta na sane da inda take.

Kara karanta wannan

Yar Najeriya Da Ta Haifi Tagwaye Ta Sake Haihuwar Yan Uku, Bidiyon Ya Dauka Hankali

A cewar Mercy, mahaifiyarta ta haifi yara 10 sannan ta bar su a wajen mahaifinta, tana mai cewa ta hadu da saurayin nata ne ta wajen mahaifinta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da take magana kan alakarta da mahaifinta, Mercy ta ce tana zuwa duba shi lokaci zuwa lokaci don sanin yadda yake.

"Ina kiran mahaifina lokaci zuwa lokaci kuma mahaifina ya san cewa ina tare da wannan mutumin."

A cewar mutumin da ke daukar bidiyon, saurayin yarinyar ya sace kokon din ubangidansa, don haka ana sa ran zai biya sannan ya bar harabar gonar.

Jama'a sun yi martani

Tuni bidiyon wanda @whiteshark_blog ya wallafa a TikTok ya yadu, inda aka samu dubban mutane da suka kalle shi sannan mutane a fadin duniya sun tofa albarkacin bakunansu.

Yayin da mutane da dama suka nuna damuwarsu a kan tsaron yarinyar da lafiyarta, wasu sun bata wajen zama idan har ta bar inda take a yanzu.

Kara karanta wannan

“Na Samu Kudi Ba Na Wasa Ba”: Budurwa Ta Taka Rawa a Wajen Jana’izar Mahaifinta, Ta Baje Makudan Kudin Da Ta Samu

@DanielAnton ya yi martani:

"Don Allah ina da gida a Najeriya kuma babu wanda ke zaune a ciki. Don Allah ina bukatar ta zauna a wajen sannan zan saka ta a makaranta ko ta koyi aiki."

@Objpaul ya ce:

"Don Allah muna iya taimakon yarinyar nan."

@user8551484400883 ya ce:

"Don Allah ku taimaketa."

@KOKO ta ce:

"Zan so na taimaka mata."

@Coolcatmarvis ta ce:

"Kawai yana so ya bata rayuwar kamar yarinyar ne. A'a haba mana don Allah."

Kalli bidiyon a kasa:

Ina so na mallaki 'ya'ya ba tare da aure ba, budurwa

A wani labarin, wata budurwa yar Najeriya, @thearabicgirl_skincare0, ta bayyana cewa ta so ta zama uwa ba tare da aure ba amma bata san yaya za ta sanar da mahaifiyarta ba.

A cewarta, ba za ta iya daukar umurni daga kowani 'da namiji ba kuma saboda haka bata tunanin yin aure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng