Yunkurin Juyin Mulki a Nijar: Tinubu Ya Gana Da Shugaban Kasar Benin, Talon, a Fadar Shugaban Kasa
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya karbi bakuncin takwaransa na kasar Benin, Patrice Talon, a fadar shugaban kasa Abuja a ranar Laraba, 26 ga watan Yuli
- Ganawar da ya gudana tsakanin shugabannin kasashen biyu baya rasa nasaba da halin da ake ciki a jumhuriyar Nijar
- Akwai yiyuwar Talon ya yiwa Tinubu, wanda shine Shugaban ECOWAS bayani kan kokarin da ake yi na dawo da tsarin dimokradiyya a yankin da ke fama da rikici
Abuja - A yanzu haka, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana cikin wata ganawa da Shugaban kasa Patrice Talon na Jumhuriyar Nijar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Talon, wanda ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 4:43 na yamma, ya kawo ziyara karo na biyu kenan a cikin mako biyu, rahoton THISDAY.
Dalilin da yasa Talon ya ziyarci shugaban kasa Tinubu
Karo na uku kenan da yake ganawa da shugaban kasa Tinubu tun bayan da ya kama mulki a matsayin shugaban kasar Najeriya, kasancewar ya hadu da shi a birnin Paris, kasar Faransa, a karshen taron kudi na duniya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ganawarsu ta yau na zuwa ne a daidai lokacin da labarai da ke fitowa daga birnin Yamai, babban birnin Jumhuriyar Nijar suka kawo cewa, wasu dakarun tsaron fadar shugaban kasar sun tsare Shugaban kasa Mohammed Bazoum.
Shugaban kasar na jumhuriyar Benin, Patrice Talon, ya ce lamarin Jumhuriyar Nijar mai makwabtaka babba ne kuma ya zama dole a gaggauta daukar mataki don ceto ta, muryar Najeriya (VON) ta rahoto.
Har ila yau, Talon ya nuna yakinin cewa idan har kungiyar ECOWAS ta gaggauta shiga lamarin za a samu sakamako mai kyau da ake bukata.
Bidiyon Dala: Kungiya Ta Tada Jijiyar Wuya, Ta Ce Bai Kamata Tinubu Ya Ba Ganduje Da Doguwa Mukamai Ba
Dakarun tsaro sun tsare shugaban kasar Nijar, Bazoum a fadar gwamnati da ke Yamai
A baya mun ji cewa dakarun tsaro sun garkame Shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum, a cikin fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai, bayan umurnin da rundunar soji ta bayar.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, majiyoyi sun ce dakarun tsaron fadar shugaban kasar sun toshe duk wata hanyar zuwa gidan shugaban kasar da ofishoshi.
Majiyoyin sun ce dogarawan sun ki sakin shugaban kasar bayan tattaunawarsu ta wargaje.
Asali: Legit.ng