ECOWAS Ba Zata Lamurci Juyin Mulki a Jamhuriyar Nijar Ba, Shugaba Tinubu

ECOWAS Ba Zata Lamurci Juyin Mulki a Jamhuriyar Nijar Ba, Shugaba Tinubu

  • Shugaba Bola Tinubu ya ce ƙungiyar ECOWAS ba zata lamurci juyin mulki a jamhuriyar Nijar ba
  • Wannan na zuwa ne yayin da rahotanni daga Nijar suka nuna cewa an rufe gidan shugaban ƙasa da wasu ofisoshinsa a Nijar
  • Tinubu, shugaban ƙungiyar ECOWAS ya ce babu wani mai ƙaunar Demokaraɗiyya da zai aminta da jurin mulkin sojoji

FCT Abuja - Shugaba ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ba za ta amince da juyin mulki a Jamhuriyar Nijar ba.

Tinubu, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ECOWAS ya bayyana haka ne a wata sanarwa da hadiminsa, D. Olusegun ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
ECOWAS Ba Zata Lamurci Juyin Mulki a Jamhuriyar Nijar Ba, Shugaba Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Rahotannin da suka fito daga Jamhuriyar Nijar da safiyar yau Laraba, 26 ga watan Yuli, 2023 sun nuna cewa an rufe fadar shugaban kasa da wasu ofisoshinsa.

Kara karanta wannan

"Tsohon Shugaban Majalisa Ya Jawowa Abdullahi Adamu Rasa Shugabacin APC"

Da yake maida martani kan wannan ci gaban, shugaban ECOWAS, Bola Tinubu ya ce ba zasu lamurci sojoji su kwace mulki a Nijar ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaba Tinubu ya ce:

"“Bayanin da ke fitowa daga jamhuriyar Nijar suna nuni da cewa wasu abubuwa marasa dadi na faruwa a kewayen shugabancin kasar."
“Ya kamata daukacin mutanen Jamhuriyar Nijar su sani cewa ECOWAS da duk masu kaunar dimokuradiyya a duniya ba za su amince da duk wani abu da zai kawar da gwamnatin da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya a kasar ba."
“Shugabannin ECOWAS ba za su amince da duk wani mataki da zai kawo cikas ga tafiyar da mulki a Jamhuriyar Nijar ko wani yanki na yammacin nahiyar Afirka ba."

Wane mataki ECOWAS zata ɗauka kan abinda ke faruwa a Nijar?

Tinubu ya ƙara da cewa a yanzu sun zuba ido suna bibiyar duk abinda ke faruwa a ƙasar Nijar kuma zasu yi mai yuwuwa wajen tabbatar da Demokuraɗiyya ta zauna daram.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Shugaban APC da Sakatare a Villa, Bayanai Sun Fito

"Muna sa ido sosai kan al’amura da abubuwan da ke faruwa a Nijar kuma za mu yi duk abin da za mu iya don tabbatar da cewa dimokuradiyya ta kafu, ta samu gindin zama, kuma ta samu ci gaba a nahiyarmu."
“Ina tuntubar sauran shugabanni a nahiyarmu, kuma za mu kare dimokuradiyyar mu bisa ka’idar tsarin mulkin kasa wanda kowa ya yarda da shi."

- Bola Tinubu.

Ya ce a matsayinsa na shugabn ECOWAS, Najeriya na tare da zababbiyar gwamnatin ƙasar Nijar kuma shugabannin Afirka ta Yamma zasu jajirce wajen kare demokuraɗiyya.

NLC: Kungiyar Kwadugo Ta Sanar da Tsunduma Yajin Aiki Daga Watan Agusta

A ɗazu kun ji cewa Kungiyar kwadugo NLC ta bayyana cewa zata tsunduma yajin aikin gama gari daga ranar 2 ga watan Agusta, 2023.

Ƙungiyar ta bai wa gwamnati mako ɗaya ta sauya waɗannan tsare- tsaren na yaƙi da talakawa ko kuma a fuskanci yajin aikin gama gari.

Kara karanta wannan

Za a Fito da Sunayen Ministoci, Gwamnoni da Tsofaffin Gwamnonin APC Sun Huro Wuta

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel