'Yan Bindiga Sun Sace Wasu Mutum 3 Da Kona Motar Jami'an Tsaro a Jihar Neja

'Yan Bindiga Sun Sace Wasu Mutum 3 Da Kona Motar Jami'an Tsaro a Jihar Neja

  • Ƴan bindiga sun sace wasu mutum uku da raunata jami'an a ƙauyen Garin Gabas na ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja
  • Miyagun ƴan bindigan sun farmakin ƙauyen ne domin satar shanu amma sai suka tarar babu shanun da za su sata
  • Gwamnan jihar Neja ya nuni alhihininsa kan harin inda ya ƙara tabbatar da cewa gwamnatinsa na yin duk mai yiwuwa domin magance matsalar tsaro a jihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Neja - Ƴan bindiga sun sake kai farmaki a Garin Gabas kusa da Yakila a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja inda suka sace mutum uku.

Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa ƴan bindigan sun raunata jami'an tsaro mutum biyu sannan suka ƙona motocinsu guda biyu.

Yan bindiga sun sace mutum uku a jihar Neja
'Yan bindigan sun kusa mutum 100 da suka farmaki kauyen Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

An tattaro cewa ƴan bindigan sun yi shirin satar shanu ne sai basu yi sa'a ba domin an kwashe shanun an kai su waje mai tsaro a Zungeru.

Kara karanta wannan

Dara Ta Ci Gida: 'Yan Bindiga Sun Sace Babban Boka Mai Bayar Da Maganin Bindiga Cikin Tsakar Dare

Hakan ya fusanta ƴan bindigan waɗannda sun kai mutum 100, suka fara harbe-harbe da ƙona kayayyakin mutanen ƙauyen ciki har da motoci biyu na jami'an tsaro waɗanda aka ajiye a jikin wata makarantar firamare inda jami'an tsaro su ke amfani da ita a matsayin sansaninsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan jihar Neja ya yi martani kan harin

Da yake martani kan harin, gwamna Mohammed Umaru Bago, ya nuna alhininsa ga masarautar Kagara kan harin inda ya yi alƙawarin kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar, rahoton Thisday ya tabbatar.

Gwamna Bago a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Bologi Ibrahim ya fitar, ya bayyana harin a matsayin abun takaici sannan ya jajantawa iyalan waɗanda harin ya ritsa da su.

Gwamnan ya roƙi al'ummar jihar da su ƙara yi wa gwamnatinsa uzuri domin baya wasa da duk wani abu dangane da kare lafiya da dukiyar al'ummar jihar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Gidan Tsohon Minista a Najeriya, Sun Tafka Barna

'Yan Bindiga Sun Farmaki Gidan Tsohon Minista

A wani labarin kuma, ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki gidan tsohon ministan watsa labarai, Labaran Maku a jihar Nasarawa.

Ƴan bindigan dai sun farmaki gidan Maku ne wanda yake a Akwanga inda suka raunata uku daga cikin masu yi masa gadi a gidan bayan sun kutsa da ƙarfin tsiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng