Gwamnatin Tarayya Za Ta Ci Tarar Masu POS Naira Miliyan 1 Kan Cajin Da Ya Wuce Ka'ida

Gwamnatin Tarayya Za Ta Ci Tarar Masu POS Naira Miliyan 1 Kan Cajin Da Ya Wuce Ka'ida

  • Gwamnatin Tarayya ta fito da sabuwar doka kan duk masu sana'ar cire kudi ta na'urar POS a kasa baki daya
  • Gwamnatin ta karkashin Hukumar FCCPC, za ta ci tarar duk wanda ya karya dokar da ta sanya tarar kudade masu yawa
  • FCCPC ta ce za ta ci kamfani tarar naira miliyan 10, yayin da za ta ci tarar kananan 'yan kasuwa miliyan daya idan suka karya dokar

Gwamnatin Tarayya karkashin Hukumar gasa da kare hakkokin kwastomomi ta tarayya (FCCPC), ta sanar da sabuwar doka kan duk masu sana'ar POS a Najeriya.

Hakan ya biyo bayan yunkurin da masu sana'ar ta POS suka yi a kwanakin baya na kara adadin kudaden da suke karba a matsayin ladar cirar kudi kamar yadda The Punch ta wallafa.

Gwamnati za ta ci tarar masu POS din da suka karya doka
Gwamnatin Tarayya za ta ci tarar masu POS din da suka saba ka'idojin da ta gindaya har naira miliyan daya. Hoto: wirestock
Asali: Getty Images

Za a ci masu kamfani tarar naira miliyan 10, marasa kamfani naira miliyan 1

Kara karanta wannan

Jihar Kano Na Kan Gaba a Yawan Wadanda Suka Kamu Da Cutar Mashako a Najeriya

Hukumar ta FCCPC ta ce duk kamfanin da aka samu ya karya dokar da ta sanya ta hana kara kudaden cirar kudin, za a ci shi tarar naira miliyan 10, mutum daya kuma tarar naira miliyan daya ko wata uku a gidan yari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mataimakin shugaban hukumar, Babatunde Irukera ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Litinin.

Ya ce hukumar ba wai tana kokarin iyakance abinda masu sana'ar ta POS za su iya karba wajen gudanar da ayyukansu ba ne, sai dai tana kokarin hana su tsawwalawa mutane kamar yadda doka ta tanada.

Hukumar ta ce ta bi duk wasu matakai na lalama kan masu POS a baya

Hukumar ta FCCPC ta kuma bayyana cewa ta bi duk wasu matakai na lalama kan masu sana'ar POS din a baya wadanda duk ba su yi tasiri ba.

Kara karanta wannan

Ahaf: Ana tsaka da yunwa a Najeriya, kwastam sun kama shinkafa da man gyaran kasar waje

Domin dabbaka doka ne hukumar ta ce ta ga ya dace ta dauki tsauraran matakai don ganin ba a saba tsarin da dokar kasa ta tanada ba wajen gudanar da kasuwancin.

Hukumar ta kuma ce duk da ba ta burin kawo cikas ga hanyar neman abincin wani, za ta dauki matakin hana wadanda suka karya dokokin na ta aiwatar da sana'ar ta POS idan hakan ya zamo dole.

A wani rahoto da The Cable ta wallafa a kwanakin baya, FCCPC ts gargadi wata kungiyar masu sana'ar POS a jihar Legas kan kara kudaden da suke karba yayin cirar kudade.

Ta ce ba burinta ba ne karya 'yan kasuwar da ke sana'ar ta cire kudade na POS, amma ya zama wajibi kowa ya yi kasuwancinsa a bisa doka.

An kama mai POS kan naira miliyan 280 da aka tura masa bisa kuskure

Legit.ng a kwanakin baya ta kawo muku labarin wani mai sana'ar POS, Alfa Rafiu da jami'an tsaro suka kama kan naira miliyan 280 da aka tura a asusunsa na banki bisa kuskure.

Kara karanta wannan

Babban Jagora a Kasar Yarabawa Ya Caccaki Tinubu Kan Wahalhalun Da Ake Sha a Najeriya

An bayyana cewa Alfa ya sha shagalinsa ne da kudin a lokacin da ya ji dirarsu a asusunsa na banki, maimakon ya yi kokarin mayarwa da mai su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng