Kano Ta Rasa Tsofaffin Kwamishinonin Ganduje 2 a Cikin Kwanaki 3

Kano Ta Rasa Tsofaffin Kwamishinonin Ganduje 2 a Cikin Kwanaki 3

  • An bayyana rasuwar tsofaffin kwamishinoni a lokacin Ganduje su biyu a cikin kwanaki uku
  • An bayyana rasuwar tsohon kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu, Alhassan Dawaki bayan fama da gajeruwar jinya
  • Haka nan an bayyana rasuwar Barista Zubaida Damakka, tsohuwar kwamishiniyar kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziƙi ta lokacin Ganduje

Kano - Jihar Kano ta yi rasa tsofaffin kwamishinoni guda biyu da suka yi aiki a gwamnatin da ta gabata ta Abdullahi Umar Ganduje, a cikin kwanaki ukun da suka gabata.

Alhassan Muhammad Dawaki, wanda tsohon kwamishina ne na ƙananan hukumomi da masarautu, da kuma Barista Zubaida Damakka, wacce tsohuwar kwamishiniyar kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki ce, sun rasu a ranar Juma'a.

Jihar Kano ta rasa tsofaffin kwamishinoni guda biyu
Jihar Kano ta rasa Alhassan Dawaki da Zubaida Damakka. Hoto: MK Ibraheem Saad, Bashir Abdullahi El-Bash
Asali: Facebook

Musabbabin rasuwar Alhassan da Zubaida

Dawaki ya rasu bayan fama da ya yi da gajeruwar jinya, wanda ya rasu yana da shekaru 79, inda kuma ya bar mata da ‘ya’ya 15 kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Makusancin Zubaida, Aminu Ibrahim, wanda tsohon babban mai taimakawa gwamna a harkokin yaɗa labarai ne, ya tabbatar da rasuwar ta ta a Abuja, bayan fama da gajeruwar jinya.

Aminu ya kuma bayyana cewa, Barista Zubaida ta rasu ta bar yara uku da kuma mijinta.

Tuni dai aka gudanar da jana'izarsu a cikin birnin Kano a ranar Lahadi kamar yadda addinin Muslunci ya tanada.

Abba Gida Gida da mataimakinsa sun yi jimamin rashin da aka yi

A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shu’aibu ya fitar, ya bayyana Dawaki a matsayin fitaccen mutumi kuma mutum ne da ake mutuntawa.

Ya kara da cewa mutuwarsa ta bar mutane da dama cikin jimami kamar yadda rahoton na Daily Trust ya bayyana.

A nasa ɓangaren, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa rasa Dawaki da aka yi ba ƙaramin rashi ba ne ga jihar Kano.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Uba Sani Ta Gano Sabuwar Cutar da Ta Ɓalle a Kaduna, Ta Faɗi Matakan da Ta Ɗauka

Gwamnan ya taya 'yan uwansa jimami, gami da yin addu'ar Allah ya ba su ikon jure wannan babban rashi da aka yi musu.

Jihar Kano ce ta fi kowace jiha yawan waɗanda suka kamu da mashako

Legit.ng a baya ta yi rahoto da ke nuni da cewa, jihar Kano ce a kan gaba wajen yawan waɗanda suka kamu da sabuwar cutar mashaƙo ta 'Diptheria'.

Hukumar daƙilie cututtuka masu yaɗuwa (NCDC), ta bayyana cewa a yanzu haka akwai mutane 819 da suka kamu da cutar a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng