Lasisin Bindiga da Kudi N300k Kadai Aka Samu a Gidan Tsohon Gwamnan CBN Emefiele, Inji Wani Lauya
- Kingdom Okere, wani shugaban lauyoyin kare dimokuradiyya, ya yi ikirarin cewa Naira 300,000 ne kadai aka samu a gidan tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele
- Okere ya kara da cewa hukumar DSS da ta kai wa Emefiele farmaki ta kuma samu lasisin harba bindiga kuma mutum kamar tsohon gwamnan CBN zai iya mallakar irin wannan kudaden da aka
- Hukumar ‘yan sandan farin kaya ta tsare Emefiele tun bayan da shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi a sati na biyu da karbar mulkin kasar nan
FCT, Abuja - Kingdom Okere, wani babban lauyan kare dimokradiyya, ya fadi a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na AriseTv cewa abin da aka gani a gidan gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele da aka dakatar bai wuce N300,000.
A baya-bayan nan ne dai aka ruwaito hukumar DSS ta kai samame gidan tsohon gwamnan babban bankin CBN, inda aka ce an bankado wasu kudade da wasu haramtattun kayayyaki a yayin samamen.
Tun bayan dakatar da shi da shugaba Bola Tinubu ya yi, Emefiele ya ci gaba da zama a hannun hukumar DSS, kuma a kwanakin baya hukumar ta bayyana cewa za a gurfanar shi da laifin mallakar makamai.
Lauya ya yi Allah wadai da kama Emefiele
Sai dai Okere ya yi Allah-wadai da tsare tsohon gwamnan na CBN, yana mai bayyana hakan a matsayin wanda ya saba wa doka kuma ya saba wa umarnin da babbar kotun tarayya na Abuja ya bayar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce abin da aka samu a gidan Emefiele kudi ne da ba su wuce N300,000 ba da kuma lasisin mallakar bindiga, inda ya kara da cewa wanda ke da matsayin kamar na Emefiele zai iya mallakar irin kudin da ma lasisin.
A cewarsa:
"Da DSS ta binciki gidan Emefiele, ta samu Naira 300,000 kacal a gidansa, shin hakan yana nufin Emefiele daga halaliyarsa na abin da yake samu ba zai iya ajiye N300,000 a gidansa ba? Da kuma lasisin mallakar bindiga, abin da kawai suka samu a gidansa kenan."
“Duk abin da Emefiele ya yi da amincewar shugaban kasa”: Lauya na so a kama Buhari
A bangare guda, an bukaci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kama tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan lamarin dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Barista Kingdom Okere ne ya yi wannan kiran yayin wata hira a shirin kalaci na Arise TV a ranar Juma'a, 14 ga watan Yuli.
Okere ya bayyana hakan yayin da yake martani ga sanarwar da DSS ta yi cewa sun gurfanar da Emefiele zuwa kotu.
Asali: Legit.ng