Yankewar Damina Ya Yi Muni, Kirista da Musulmi Sun Yi Addu’o’in Rokon Ruwa a Jihar Borno
- Yayin da gonaki ke ci gaba da lalacewa a Arewacin Najeriya, an fita addu’o’in rokon ruwa a jihar Borno
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, Musulmai da Kirista ne suka fita addu’o’in rokon ruwa a jihar
- Shehun Borno ya yi kira ga mazauna jihar da su koma ga Allah don neman rahama da amfanin gona
Jihar Borno - Musulmi da Kirista sun gudanar da addu’o’in rokon samun ruwan sama da kuma ci gaban zaman lafiya a jihar Borno.
Jama’a da dama ne suka taru a Maiduguri babban birnin jihar domin yin addu’ar rokon ruwan sama a yayin da ake fama da fari a sassan jihar.
An ruwaito cewa, an yi sallar rokon ruwa a masallatan Juma'a da dama a jihar, kana aka gudanar addu'o'i a cocin Baptist da birnin Maiduguri a ranar Lahadi.
Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa
Kiran da aka yiwa ‘yan Borno
An yi kira ga mabiya addinin Islama da Kirista a jihar ta Borno da su koma ga Allah, kana su roki Allah ya dawwamar da zaman lafiya da saukar ruwa a jihar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Haka nan, an roki masu karfi da su taimaki na kasa, tare da tallafawa talakawa mabukata a fadin jihar.
Ya kuma shawarci iyaye da su rika yiwa ’ya’yansu nasiha a kan ayyukan assha kamar shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran munanan dabi’u.
Hakazalika, ya shawarci ‘yan kasuwa su ji tsoron Allah wajen mu’amalarsu ta kasuwanci tare da tausayin na kasa, rahoton Aminiya.
Bayanan malaman addinin Kirista
Da yake bayani yayin taron addu’o’in Kiristocin da aka gudanar a cocin Baptist, Shugaban CAN na Jihar Borno, Reverend John Bakeni, ya roke su da su nemi rahamar Ubangiji tare da binSa wajen gudanar da ayyukansu.
Har ila yau, limamin cocin Anglican na Maiduguri, Reverend Emmanuel Morris, ya yi addu’ar Allah ya ba wa jihar zaman lafiya mai dorewa da ruwan sama mai albarka domin amfanin gona.
Gwamna da kan shi ya jawo jama'a zuwa Sallar rokon ruwa saboda yankewar damina
A wani labarin, gwamna Bala Abdulqadir Mohammed na jihar Bauchi, ya jagoranci mutane a wurin sallar rokon ruwa a ranar Alhamis.
Daily Trust ta tabbatar da cewa Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi yana cikin wadanda su ka bi wannan sallah ta musamman.
Da yake jawabi bayan an idar da sallar, Bala Abdulqadir Mohammed ya ce sun dade su na sa ran ruwan sama a har yanzu bai sauko ba.
Asali: Legit.ng