Yan Bindiga Sun Farmaki Gidan Tsohon Minista a Jihar Nasarawa, Sun Raunata Masu Gadi Mutum Uku

Yan Bindiga Sun Farmaki Gidan Tsohon Minista a Jihar Nasarawa, Sun Raunata Masu Gadi Mutum Uku

  • Ƴan bindiga sun kai farmaki gidan tsohon ministan watsa labarai, Labaran Maku ɗake a jihar Nasarawa
  • Ƴan bindigan waɗanda suka kutsa cikin gidan da ƙarfin tsiya sun raunata mutum uku daga cikin masu gadin gidan
  • Toshon ministan ya koka kan yadda ake farautar rayuwarsa inda ya ce wannan ne karo na uku da ƴan bindiga ke kawo masa hari a cikin wata ɗaya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Nasarawa - Ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun farmaki gidan tsohon ministan watsa labarai, Labaran Maku, ranar Asabar da daddare inda suka raunata masu gadi mutum uku.

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa ƴan bindigan waɗanda suka yi ta harbe-harben bindiga, sun kutsa kai cikin gidan Maku dake a Ola cikin ƙaramar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa da misalin ƙarfe 7:50 na dare.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Kauyukan Jihar Bauchi Sun Halaka Mutum Biyu Da Yin Awon Gaba Da Wasu

Yan bindiga sun kai farmaki gidan Labaran Maku
Yan bindigan sun kutsa cikin gidan da ƙarfin tsiya Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Ɗaya daga masu gadin wanda ya raunata ya bayyana cewa maharan waɗanda suka yi magana cikin harshen Hausa sun yi ta dukan ƙofar gidan kafin su hauro ta katanga bayan sun fahimci cewa babu wanda zai buɗe musu gidan.

A kalamansa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Lamarin akwai tashin hankali a ciki. Sun zo ne da yawa inda suka riƙa dukan ƙofar suna magana da Hausa, amma lokacin da muka fahimci baƙin fuska ne sai muka ƙi buɗe musu ƙofar."
Saboda ƙin buɗe musu ƙofar da muka yi shine sai suka fara harbe-harbe sannan daga baya suka hauro cikin gidan ta katanga, inda suka raunata mu yayin da mu ke ƙoƙarin magance lamarin."

Maku ya koka kan yadda ƴan bindiga ke farautar rayuwarsa

Da yake magana kan lamarin, tsohon ministan watsa labarai, Labaran Maku ya koka cewa wannan ne karo na uku da cikin wata ɗaya da ƴan bindiga su ke kai masa hari a gida, rahoton Nigerian Tribune ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hankula Sun Tashi Bayan Wata Katanga Ta Rufto Kan Wasu Yara, An Samu Asarar Rai

"Idan ba ku manta ba kusan wata ɗaya da wuce sun farmaki gidan mahaifina a Wakama inda suka sace ƙannena guda uku." A cewarsa.
"Ɗayan lokacin kuma sun halaka ƴaƴan yayana guda biyu nan take a cikin gida."

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar ba, DSP Ramhan Nansel, saboda bai amsa kiran da aka yi masa a waya ba.

'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Biyu a jihar Bauchi

A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun halaka wasu mutum biyu a wani farmaki d asuka kai a ƙauyen Tamba na ƙaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.

Ƴan bindigan sun kuma yi garkuwa da wasu mutum biyu a ƙauyen dake maƙwabtaka da Tamba duk a cikin ƙaramar hukumar ta Ningi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng