Jihar Kano Na Kan Gaba a Yawan Wadanda Suka Kamu Da Cutar Mashako a Najeriya

Jihar Kano Na Kan Gaba a Yawan Wadanda Suka Kamu Da Cutar Mashako a Najeriya

  • Yayin da ake ci gaba da jimami, hukumar NCDC ta bayyana jihar Kano a matsayin inda ya fi ko’ina yawan masu cutar mashako
  • Hukumar dakile yaduwar cututtuka masu harbuwa ta ce mutane 836 ne suka harbu da cutar kuma ciki Kano na da 819
  • Cutar dai na kama mutum a makogaro ne inda zai dunga ji kamar an shakure masa wuya

Kano - Hukumar dakile yaduwar cututtuka masu harbuwa ta NCDC, ta bayyana cewa cutar mashako wacce ake ce ma 'diphtheria' a turance ta halaka mutane 80 a Najeriya tsakanin watan Mayu da Yunin 2023.

Kamar yadda ya bayyana a rahoton da hukumar NCDC ta fitar, yanzu haka mutane 836 ne suka kamu da cutar kuma jihar Kano ce ke da mafi rinjayen masu cutar wanda yawansu ya kai 819.

Kara karanta wannan

Ahaf: Ana tsaka da yunwa a Najeriya, kwastam sun kama shinkafa da man gyaran kasar waje

Abba Kabir Yusuf
Jihar Kano Na Kan Gaba a Yawan Wadanda Suka Kamu Da Cutar Mashako a Najeriya Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Alkaluman sun shafi kananan hukumomi 33 na jihohi bakwa da suka hada da Yobe da Katsina da Sokoto Zamfara da Kaduna da babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda hukumar ta sanar.

Wannan abun tashin hankali ne sosai, tsohon shugaban NCDC

A hirarsa da sashin Hausa na BBC, tsohon shugaban hukumar ta NCDC, Farfesa Abdussalam Nasidi, ya bayyana halin da ake ciki a matsayin abun tashin hankali matuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Farfesa Nasidi, ya zama wajibi a dauki mataki idan ba haka ba za a sha kunya.

Ya kuma bayyana cewa idan har mutum ya kamu da cutar to ba lallai ne rigakafin ya yi masa aiki ba, musamman ma ganin cewa a yanzu ana fama da karancin rigakafin.

Cutar mashako na kama mutane a makogaro

Babban masanin kiwon lafiyan ya kuma bayyana cewa cutar mashako yana riskar mutum a makogaro ne, inda take hana shi sukuni

Kara karanta wannan

Tallafin Tinubu: “Rabon N8,000 Duk Yaudara Ce”, Gwamnan Kaduna Ya Fadi Dalili

Ya ce: ''Idan ta kama mutum za ta rike masa wuya yadda zai dunga ji kamar an shake shi, idan ta kama yaro idan ba Allah ne ya kiyaye ba a gaban iyayensa za a rasa shi, don haka babban barazana ce''

Gwamnatin Kaduna Ta Tabbatar da Bullar Cutar Mashako a Kafanchan

A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnatin Kaduna karkashin gwamna Malam Uba Sani ta tabbatar da ɓullar cutar 'Diphtheria' watau Mashaƙo a wasu kauyukan Kafanchan, karamar hukumar Jema'a.

Ma'aikatar lafiya ta jihar Kaduna ce ta tabbatar da ɓullar cutar bayan rahotannin da aka samu cewa mazauna gundumomin Takau, Kafanchan A da Kafanchan B sun kamu da wata sabuwar cuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng