Mutum Shida Sun Mutu Bayan Kwankwadar Barasa a Jihar Ogun

Mutum Shida Sun Mutu Bayan Kwankwadar Barasa a Jihar Ogun

  • Wasu mutum shida sun yi bankwana da duniya bayan sun sha barasa a jihar Ogun da ke yankin Kudu maso Yamma
  • Mutanen dai sun kwankwaɗi barasar ne wacce abokinsu ya kawo musu amma shi sai ya ƙi shan barasar
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa mutumin da ya kawo musu barasar ya ranta ana kare bayan samun labarin mutuwarsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ogun - Mutum shida sun mutu bayan sun sha barasa da ake zargin abokinsu ne ya basu a Ogbogbo, cikin ƙaramar hukumar Ijebu ta Arewa maso Gabas a jihar Ogun.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne a ranar Talata a wani wurin shan iska inda wasu abokai mutum bakwai suka taru domin sararawa.

Mutum shida sun mutu bayan shan barasa a jihar Ogun
Wanda ya basu barasar dai ya ranta ana kare Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Majiyoyi sun bayyana cewa dukkanin mutum shidan da suka sha barasar sun mutu banda ragowar mutum na bakwai ɗin wanda ya kawo barasar daga gida amma bai kwankwaɗa ba.

Kara karanta wannan

"Muna Jin Jiki": Gwara Gwamnatin Buhari Akan Gwamnatin Tinubu, Wata Mabaraciya Ta Magantu

Sun yi gardama a tsakaninsu

Mutanen da suka riga mu gidan gaskiya da wanda ake zargin dai sun yi zazzafar gardama wacce daga baya suka sasanta, rahoton The Cable ya tabbatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyar wanda ya nemi da a sakaya sunansa ya bayyana cewa wanda ake zargin ya nemi da ya bayar da kyautar kwalbar barasa ɗaya domin nuna cewa komai ya wuce bayan gardamar da suka yi.

Wanda ake zargin daga nan sai ya je gida ya ɗauko barasar ya basu inda su duka suka kwankwaɗa banda shi.

Ƴan sa'o'i kaɗan bayan sun bar wajen sun koma gidajensu, labari sai ya karaɗe garin cewa mutum biyu daga cikinsu sun mutu yayin da aka kwantar da mutum huɗu a asibiti.

Majiyar ya bayyana cewa daga baya ragowar mutum huɗun sun mutu washe gari, yayin da wanda ake zargin ya cika wandonsa da iska.

Kara karanta wannan

Tallafin Man Fetur: Taliya, Gari Da Rukunin Abubuwa 5 Da Zaka Iya Saya Da Naira 8,000

Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Omolola Odutola, ta tabbatar da aukuwar lamarin. Sai dai, ba tace komai ba dangane da yawan mutanen da suka mutu.

"Eh na samu labarin wani abu makamancin wannan ya auku amma iyalansu sun ce ba za su shigar da ƙara ba sun gwammace su binne gawarwakin." A cewarta.

'Yan Sanda Sun Tsare Matashi Kan Zargin Halaka Mahaifiyarsa

A wani labarin kuma, ƴan sanda sun yi caraf da wani matashi wanda ake zarginsa da halaka mahaifiyarsa har lahira a jihar Ogun.

Ƴan sandan sun bayyana cewa matashin da ake zargin ya dai shaƙe wuyan mahaifiyar tasa ne har sai da ta mutu bayan ya sha miyagun ƙwayoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng