Al’ummar Bauchi Sun Zargi Sarakunan Gargajiya Da Kwace Masu Filaye
- Al'ummar kauyen Tulu da ke yankin Lame ta karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi sun koka a kan fin karfin da mai unguwar Tulu yake masu
- Mazauna yankin Tulu sun zargi mai anguwar da hakimin kauyen da hada kai wajen kwace masu gonaki da filayensu sannan su siyar wa wasu
- Sai dai, hakimin garin, Alhaji Adamu Yakubu, ya karyata zargin inda ya ce babu hannunsa a cikin wannan sabgar da ake zarginsu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Bauchi - Wasu mazauna kauyen Tulu da ke yankin Lame ta karamar hukumar Toro a jihar Bauchi sun zargi mai anguwar Tulu da kwace masu filayensu don amfanin kansa.
Al'ummar yankin sun yi zargin cewa mai anguwar yana hada kai da hakimin kauyen Tulu wajen aiwatar da aika-aikar da ake zarginsa a kai, Daily Trust ta rahoto.
Daya daga cikin wadanda abun ya cika da su, Alhaji Shehu Yerima Tulu, ya yi jawabi ga manema labarai a madadin mazauna yankin da abun ya shafa.
Yerima Tulu ya ce tsarin da mai anguwar, Tashan Tulu yake amfani da shi shine zai zo ya duba gonakin da suka yi masa sai ya yi ikirarin cewa mallakinsa ne.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Ya yi irin haka ga mazauna garin Tulu da dama ta hanyar kwace masu gonakinsu da filaye ta karfin tuwo sannan ya siyar wa wasu."
Ya ce akalla mutanen garin 25 ne abun ya ritsa da su.
Hakimin kauyen Tulu ya yi martani
Da aka tuntube shi, hakimin kauyen Tulu, Alhaji Adamu Yakubu, ya karyata dukkanin zarge-zargen na kwace gonaki da mallakar su ba bisa ka'ida ba, inda ya ce sam shi baya daga cikin wannan.
Ba zan yafe maka ba: Fati Muhammad ta yi martani ga mutumin da ya yi mata kazafi
A wani labari na daban, mun ji cewa fitacciyar tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Muhammad ta mayar da martani ga wani mutum da ya yi mata zafafan kalamai a dandalin soshiyal midiya.
Mutumin dai ya yi mara zagin kare dangi da cin mutunci sannan ya kuma kira ta da mayya.
Ta bayyana cewa ita ba sauran askarawa bace domin bata taba zaman kasar Saudiyya ba sai dai ta je hajji da Umurah.
Asali: Legit.ng