Da Dumi-Dumi: Wasu Yara Sun Riga Mu Gidan Gaskiya Bayan Katanga Ta Rufto Musu a Jihar Legas
- Wata katanga ta ruftowa gidan dake makwabtaka da ita inda ta yi ajalin wasu ƙananan yara guda biyu a jihar Legas
- Katangar dai ta rufto ne a dalilin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka tafka a yankin Isawo cikin ƙaramar hukumar Ikorodu ta jihar Legas
- Yaran sun rasu ne bayan sun maƙale a ɓuraguzan katangar da ta rufto musu inda sai da aka kwashe dogon lokaci ana ƙoƙarin ceto su
Jihar Legas - Wasu ƙananan yara guda biyu, Gbolahan da Olayinka Atolagbe, sun riga mu gidan gaskiya bayan katangar wani gida dake maƙwabtaka da na su ta rufto musu a jihar Legas.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa lamarin ya auku ne a lokacin wani ruwan sama mai kama da bakin ƙwarya da aka tafka ranar Asabar, a titin Alao, cikin Isawo a ƙaramar hukumar Ikorodu ta jihar.
Yanzu-Yanzu: Karshen 'Yan Bindiga Ya Zo, Hukumar Sojojin Kasa Ta Kaddamar Sabon Atisayen Kakkabe Miyagu
An ciro gawarwakin yaran a cikin ɓuraguzan katangar bayan sun kwashe sa'o'i masu yawa yayin da ake ta ƙoƙarin ceto su, cewar rahoton Tribune.
Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin
Kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) yankin Kudu maso Yamma, Mr Ibrahim Farinloye, ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Lokacin da aka tuntuɓi wata jami'ar hukumar kwana-kwana ta jihar Legas, ta tabbatar da aukuwar lamarin amma ta bayyana cewa ba za ta iya bada cikakkun bayanai ba, saboda ba ta samu cikakken rahoto ba kan ƙoƙarin ceto yaran da aka yi.
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na janyo rushewar gidaje musamman waɗanda basu da ƙwari ko suka tsufa a dalilin lafkewar da ruwan yake sanyawa su ke yi.
A jihar Legas ana yawan samun rushewar gine-gine musamman benaye waɗanda ake aikin gina su ko waɗanda suka tsufa.
NULGE: Jerin Sunayen Gwamnonin Jihohi 16 Da Har Yanzu Ba Su Aiwatar da Mafi Karancin Albashi N30,000 Ba
Bene Mai Hawa Uku Ya Rufto a Jihar Delta
A wani labarin na daban kuma, wani ginin bene mai hawa uku da ba a kammala ba ya ruguje a ƙaramar hukumar Oshimili ta jihar Delta.
Ginin benen wanda rahotanni suka tabbatar na wani otal ne dai ya ruguje ne a yankin Okotomi, Okpanam na ƙaramar hukumar Oshimili.
Asali: Legit.ng