“Na Tara Kudi Sosai”: Budurwa Yar Shekaru 19 Wacce Ta Siya Siminti Da Bulo a Hankali a Hankali Ta Gina Daki 1

“Na Tara Kudi Sosai”: Budurwa Yar Shekaru 19 Wacce Ta Siya Siminti Da Bulo a Hankali a Hankali Ta Gina Daki 1

  • Wani dan gajeren biyon wata budurwa wacce ta gina daki daya a shekaru 19 ya karfafawa mutane da dama gwiwa yayin da suka jinjina mata
  • Matashiyar ta bayyana cewa ta fara siyan kayan gini tun tana da shekaru 18 kuma dole ta hakura da kayan alatu da yawa
  • A cewarta, ta kan koka wasu lokuta kan abubuwan da take sadaukarwa don ganin ta mallaki gida

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiyar budurwa yar shekaru 19 ta yi bidiyon yadda ta mallaki gida nata na kanta tana da karancin shekaru.

Matashiyar (@im.moody.bby1) ta ce sai da ta tara dukka kudadenta don siyan siminti da bulo don gina gidan mai daki daya.

Matashiya ta gina daki daya da guminta
“Na Tara Kudi Sosai”: Budurwa Yar Shekaru 19 Wacce Ta Siya Siminti Da Bulo a Hankali a Hankali Ta Gina Daki 1 Hoto: @im.moody.bby1
Asali: TikTok

Gida mai daki daya da ya sha tayil

Da take nuna cikin gidan da hadadden tayil, matashiyar ta ce takalmi daya ke gareta da silifas biyu sannan bata da gashin kanti. Ta kara da cewar ta gwammaci mallakar gida da za ta kasance cikin kwanciyar hankali fiye da yin rayuwar karya a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Budurwa Tana Dafa Taliya Da Lemun Mirinda Da Sukari Ya Girgiza Intanet

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan kammala gidan, matashiyar ta samu kayan wutanta da kayan daki a hankali a hankali. A wani bidiyon, matashiyar ta ce ta samu kudinta ne daga wata sana'a da ta fara tana da shekaru 17.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Ebony flame ta ce:

"Jinjinata a gareki. Kana ki daina abun da kike yi sannan ki fuskanci inda kika sa gaba."

davioclarke ya ce:

"Ina matukar alfahari da ke a matsayinki na matashiya."

kay-Andy ya ce:

"Allah ya rubanya dakinnan zuwa dakuna. Ina hango maki wannan. za ki yi nisa."

Riska ta ce:

"Ina matukar mutunta ki..Ina son wannan, ki ci gaba da zuwa."

Boss chin ta ce:

"Ina alfahari da ke haka nima na fara a rayuwata tun ina 18, kuma da wannan kudirin za ki cimma nasara da wuri a rayuwa a farkon shekaru 20."

Kara karanta wannan

“Bai Taba Cin Amanata Ba”: Budurwa Ta Ki Amsa Tayin Saurayin Da Suka Shafe Shekaru 8 Suna Soyayya, Ta Fadi Dalili

Budurwa ta ginawa kanta gidan kwano mai daki 1

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa wata budurwa ta garzaya Twitter domin baje kolin dan karamin gidan da ta ginawa kanta.

Budurwar mai suna Thaidzo, ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta ce a karshe ta zama mai gidan kanta a shekaru 19.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng