Emefiele: Za'a Gurfanar da Dakataccen Gwamnan CBN a Gaban Kotu

Emefiele: Za'a Gurfanar da Dakataccen Gwamnan CBN a Gaban Kotu

  • Ranar Talata 25 ga watan Yuli, 2023 za a gurfanar da dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele a gaban babbar kotun tarayya
  • Alkalin Kotun, mai shari'a Nicholas Oweibo ne ya sanya ranar bayan warware ruɗanin da aka samu daga hukumar DSS
  • Hukumar 'yan sandan farin kaya na tuhumar Mista Emefiele da mallakar bindiga da alburusai da bisa ƙa'ida ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos - Babbar Kotun tarayya mai zama a jihar Legas ta sanya ranar 25 ga watan Yuli, 2023 a matsayin ranar da za a gurfanar da dakataccen gwamnan babban banki (CBN), Godwin Emefiele.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa za a gurfanar da Emefiele a gaban Kotun ne domin fuskantar shari'a kan tuhumar mallakar haramtattun makamai.

Za a fara shari'ar dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Emefiele: Za'a Gurfanar da Dakataccen Gwamnan CBN a Gaban Kotu Hoto: CBN
Asali: UGC

Alkalin Kotun mai shari'a Nicholas Oweibo ne ya sanya ranar fara sauraron ƙarar bayan jinkirin hukumar yan sandan farin kaya (DSS) wajen gabatar da tuhume-tuhume kan wanda ake zargi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shetimma, Gwamnoni da Sauran Mambobin NEC Sun Sa Labule a Villa, Bayanai Sun Fito

A ranar 13 ga watan Yuli, 2023, hukumar DSS ta shigar da tuhume-tuhume biyu kan Emefiele a Kotun wanda suka ƙunshi mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wane zargi DSS take wa Emefiele?

A tuhumar da DSS ta shigar gaban babbar kotun tarayya, hukumar ta zargi Emefiele da mallakar ƙaramar bindiga (JOJEFF Magnum 8371) mara lasisi.

Haka nan kuma hukumar ta zargi dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya da mallakar alburusai 123 waɗanda ba su da lasisin haƙƙin mallaka kamar yadda doka ta tanada.

Waɗannan tuhume-tuhume guda biyu sun saɓa wa sashi 4 da na 8 a dokar mallakar bindiga Cap F28 2004 kuma babban laifi ne a karƙashin saahi na 27 (1)(b)(i) na kundin dokar.

Tun yauahe DSS ke tsare da Emefiele?

Mista Emefiele ya shiga hannun DSS ne tun bayan lokacin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da shi daga matsayin gwamnan CBN, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jimami Yayin da Dan Takarar Majalisar Tarayya a Arewa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Jami'an DSS sun titsiye Emefiele a ofishinsu tsawon lokaci kafin daga bisani suka shigar da ƙara kan zargin da ake masa gaban babbar kotun tarayya mai zama a Legas.

Wani lauya masanin doka, Barista Tukur Badamasi, ya zanta da Legit.ng Hausa, ina ya ce ita shari'a saɓanin hankali ce, komai ka iya faruwa gabannin a yanke hukunci.

A cewar lauyan, DSS zata yi kokarin tabbatar da tuhumar da take wa dakataccen gwamnan yayin da shi kuma da tawagar lauyoyinsa zasu yi kokarin wanke shi daga zargi.

Lauyan ya shaida wa wakilin mu cewa:

"Ita shari'a kafin a fara ba zaka ce ga wanda zai yi nasara ba, kowane ɓangare zai yi kokarin gamsar da Kotu shi ke da gaskiya, amma daga karshe alkali zai yanke hukunci daidai da hujjojin da ya tattara."
"Zargin da ake masa (Emefiele) babban laifi ne saboda haka shari'ar zata ja hankali duba da shi kansa da matsayin da ya rike, yanzu dai mu sa ido mu ga yadda zata kaya."

Kara karanta wannan

Emefiele: Dakataccen Gwamna CBN Ya Gabatar da Muhimmiyar Buƙata 1 a Gaban Kotu, Ya Faɗi Dalilai 9

Abba Gida Gida Ya Kawo Tsaiko a Zaman Sauraron Karar Zaben Gwamnan Kano

A wani rahoton kuma yayin ci gaba zaman sauraron ƙarar zaben gwamnan jihar Kano ranar Jumu'a, gwamna Abba Kabir Yusuf ya kawo cikas.

Rashin halartar shaidu 3 da gwamnan ya shirya gabatarwa ya tsaida zaman har Kotu ta ɗage zuwa 22 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262