"N8,000 Kudi Ne Masu Yawa" Gwaman Sule Ya Kare Tallafin Shugaba Tinubu
- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce N8,000 kuɗi masu yawa a wurin wasu iyalai da yawa masu fama da talauci
- Sule ya ce mai yiwuwa kuɗin ba su taka kara sun karya a wurin wasu ba, amma wasu magidantan ba su iya samun haka a wata guda
- Gwamnatin tarayya na shirin raba wa miliyoyin iyalai N8,000 duk wata a tsawon watanni 6 domin rage musu zafin cire tallafin man fetur
Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya kare shirin gwamnatin tarayya na raba wa magidanta N8,000 domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur a Najeriya.
Gwamna Sule ya yi ƙarin haske kan tallafin N8,000 ne yayin da ya bayyana a cikin shirin siyasa a yau na kafar watsa labaran Channels tv ranar Jumu'a.
Ya ce Naira 8,000 kuɗi ne masu yawa ga iyalai da dama da ke fama da talauci wadanda ba kasafai su ke iya samun irin wannan kuɗi ba a cikin wata guda.
Gwamnan ya tunatar da cewa iyalai da yawa ne suka ci gajiyar N5,000 da aka raba a baya a matsayin tallafi, yana mai cewa matakin na yanzu ya yi daidai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
N8,000 zasu yi tasiri ga iyalai da dama - Sule
Daily Trust ta rahoto gwamna Sule na cewa:
"A baya mun raba N5,000 ne kawai kuma na yi imanin cewa akwai mutane da yawa da ke jiran wannan N5,000 duk wata."
"Lallai akwai wasu yankuna a ƙasar nan da suka iya ba da gudummawarsu kuma sun iya yin abubuwa da yawa a cikin al’ummominsu daban-daban.”
“N8,000 ba komai bane ga wasu mutane, amma kuɗi ne masu auki ga wasu da yawa daga cikin iyalai marasa galihu da ba sa ganin N8,000 duk wata. Don haka, abu guda kawai shi ne mu tantance wadannan iyalai.”
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin sake duba kudin tallafin Naira 8,000 biyo bayan harzuka da mutane suka yi a fadin kasar nan.
Abba Gida Gida Ya Kawo Babban Cikas a Zaman Sauraron Ƙarar Zaben Gwamnan Kano
A wani rahoton kun ji cewa rashin halartar shaidun gwamna Abba Kabir Yusuf a zaman ci gaba da sauraron ƙarar zaben gwamnan Kano ya kawo cikas.
Yayin ci gaba da zaman sauraron ƙarar ranar Jumu'a, lauyan Abba Gida-Gida, Eyitayo Fatigun (SAN), ya shaida wa Kotu cewa sun tanadi shaidu uku da zasu gabatar.
Asali: Legit.ng