Jami’ar Danfodiyo Ta Dage Jarrabawa Saboda Rashin Biyan Kudin Makaranta
- Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto ta sanar da sabon rana da za a fara jarabawar zangon karatu na farko
- Makarantar ta bayyana cewa an dage jarrabawar na tsawon mako guda kuma yanzu za a fara a ranar 31 ga watan Yuli
- An dage jarrabawar zangon karatun na farko ne saboda rashin biyan kudin makaranta daga bangaren dalibai
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Sokoto - Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ta dage jarabawarta na zangon karatu na farko a kalandar 2022/2023 da mako guda.
Da yake jawabi ga jaridar Nigerian Tribune, shugaban kula da harkokin dalibai, Farfesa Umar Aliyu, ya ce an dage jarrabawar ne saboda rashin biyan kudin makaranta daga bangaren dalibai, inda ya ce wannan shi ne karo na hudu da ake dage jarrabawar wannan zangon karatun.
"Menene dalilin da yasa dalibai kan isa garemu ne a lokacin da ya rage yan mintoci kafin karewar wa'adin da aka diba?
"Wannan shine karo na hudu da ake tsawaita wannan rijistan," inji shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalibai sama da 10,000 basu yi rijista ba
Aliyu ya yi bayanin cewa an tilasta wa makarantar tsawaita wa’adin rufe rajistan saboda har yanzu dalibai sama da dubu goma ba su biya kudin makarantarsu ba.
"Zuwa yau, fiye da dalibai dubu goma sun gaza yin rijistan wannan zangon karatun."
Shugaban kula da dalinam ya bayyana cewa an dage jarrabawar zangon karatu na farko zuwa ranar 31 ga watan Yuli sannan duk dalibin da ya ki amfani da wannan dama bai da wani zabi da ya wuce jingine admishan din.
"Babu yadda za a yi mu tsawaita tsarin rijistan da ba zai shafi jarrabawar ba. Son haka, sabon sati na rijista ne sannan satin sama zai zama na jarrabawa.
"Idan wadannan dalibai suka yin rijista a cikin mako dayan da aka kara, dole su jingine admishan dinsu."
Matashi ya nemi mai yi masa wanki ya dawo masa da N80 da ya tsinta a aljihunsa
A wani labarin, wani mutumin ya bukaci mai yi masa wanki da guga da ya gaggauta dawo masa da kudin da ya tsinta a aljihunsa yayin da yake wanke masa kaya.
Mai wanki da gugan ya tsinci N80 a aljihun kwataman nasa sannan ya sanar da shi ta Whatsapp.
Asali: Legit.ng