Dan Majalisar Tarayya Daga Edo Ya Gamu da Hatsari a Hanyar Zuwa Abuja
- Hatsarin mota ya rutsa da ɗan majalisar tarayya daga jihar Edo, Marcus Onobun, a hanyarsa ta koma wa birnin tarayya Abuja ranar Laraba
- Shugaban PDP reshen jihar Edo, Tony Aziegbemi, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ɗan majalisar yana cikin hayyacinsa amma ya samu karaya a jikinsa
- Sakataren watsa labaran Honorabul Marcus Onobun, ya ce mai gidansa ba ya cikin mummunan yanayin da za a damu
Edo state - Ɗan majalisar wakilan tarayya kuma tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Marcus Onobun, ya gamu da hatsarin mota ranar Laraba da ta gabata.
Hatsarin ya rutsa da ɗan majalisar a Ekpoma-Auchi wani ɓangaren titin Benin zuwa Abuja yayin da yake kan hanyar koma wa Abuja domin halartar zaman majalisa.
Daily Trust ta ce ya kamata Honorabul Onobun ya koma Abuja ta jirgin sama amma rahotanni sun ce ya rasa jirginsa, bisa haka ya yanke shawarar tafiya ta mota.
An tattaro cewa dan majalisar mai wakiltar mazaɓun Esan ta Yamma, Esan ta tsakiya da kuma Igueben a majalisar wakilai ta ƙasa, ya samu rauni a hatsarin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bayanai sun nuna motar ɗan majalisar ta yi kaca-kaca a hatsarin wanda suka yi taho mu gama bayan ya bugi wani rami a kan titin.
Jam'iyyar PDP ta tabbatar da faruwar haɗarin
Shugaban Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Edo, Tony Aziegbemi, ya tabbatar da faruwar hatsarin.
Mista Aziegbemi ya ce ɗan Majalisar na cikin hayyacinsa kuma ya samu damar yin magana da shi lokacin da ya kai masa ziyara.
A rahoton jaridar Punch, Shugaban PDP ya ce:
"Eh tabbas ya yi hatsari ranar Laraba kuma ya samu karaya a wasu ɓangarorin jikinsa amma yana karkashin kulawar likitoci kuma ba ya cikin mummunan yanayi."
Sauƙi Ya Zo: Gwamnatin Tinubu Zata Karya Farashin Abinci a Jihohi, Ta Bada Sabon Umarni Ga NEMA da CBN
Har ila yau, babban sakataren watsa labaran ɗan majalisar tarayyan, Adodo Ebojele, ya tabbatar da lamarin, ya ce tsohon kakakin majalisar dokokin yana cikin hayyacinsa.
Jerin Sunayen Sarakunan da Gwamnatin Bauchi Ta Tsige Kan Zarge- Zarge 2
A wani labarin na daban Gwamnatin Bauchi ta kori Sarakuna 6 daga kan karagar mulki bisa laifin shiga siyasa, rashin ɗa'a da wasu laifuka.
Mun haɗa muku jerin sunayen Sarakunan da korar ta shafa waɗanda ke karkashin masarautar Bauchi da masarautar Katagum.
Asali: Legit.ng