“Ka Turo Mun Lambar Suga Momina”: Matashi Ya Roki Barawon Da Ya Sace Masa Waya
- Wani mutumin Kisii ya ba da labarin halin da ya shiga bayan ya rasa wayarsa a yayin zanga-zangar Azimio
- Mutumin ya tuntubi TUKO.co.ke yana mai ikirarin cewa yana cikin aikin zanga-zanga ne lokacin da barawo ya sace masa waya
- Yana rokon barawon da ya bude wayarsa ta hanyar amfani da lambobin sirri 409649 sannan ya aika masa da lambar wata mata da ke biyan kudin hayarsa
Wani matashi mai suna Silvanus, na neman lambar wayar masoyiyarsa a kan wata wayarsa da ta bata a lokacin da ya bi sahun sauran mutanen Kenya a zanga-zangar kin jinin gwamnati da shugaban ODM Raila Odinga ya shirya.
Matashi baya biyan kudin hayar gidansa
Silvanus ya ce yana ta kokarin samun lambar 'suga momin' amma abun ya ci tura.
Mutumin ya tuntubi kafar labarai ta kasar Kenya, TUKO.co.ke ta wayar abokinsa, yana mai ikirarin cewa ya rasa wayarsa a yayin wata zanga-zanga da ya halarta a ranar Laraba, 19 ga watan Yuli.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An shirya yin zanga-zangar ne na tsawon kwanaki uku daga ranar Laraba, 19 ga watan Yuli zuwa ranar Juma'a, 21 ga watan Yuli.
Silvanus ya bayyana cewa matar ce ke biyan kudin hayarsa, kuma zai so barawon ya tura masa lambarta ta shafinsa na Facebook.
Ya bayyana cewa ya sakawa matar suna 'Mercy my suga' a waya kuma lambobin sirri na bude wayar shine 409649.
Ya ce:
"Jiya, ina zanga-zanga a garin Kisii, sai aka sace mun wayata, sannan akwai wata mata da kan taimaka mani da bukatuwa na kudi. Ita ce ke biyan kudin hayar gidana a nan. An sace wayar, kuma ba ni da lambarta. Don haka ina neman ku yada mani wannan. Lambar da nake kiranku da ita yanzu ba nawa bane. Na daya daga cikin abokaina ne."
Budurwa ta dafa taliya da lemun mirinda da sukari a bidiyo
A wani labarin, mun ji cewa wata matashiyar budurwa ta sha caccaka a soshiyal midiya bayan ta hada wasu sinadarai masu ban al'ajabi wajen girka abincinta.
Matashiyar dai ta dafa taliya ne ta hanyar amfani da lemun mirinda sannan ta barbada sukari a ciki.
Asali: Legit.ng