Jerin Sunayen Sarakunan da Gwamnatin Bauchi Ta Tsige Kan Zarge-Zarge 2

Jerin Sunayen Sarakunan da Gwamnatin Bauchi Ta Tsige Kan Zarge-Zarge 2

  • Gwamnatin jihar Bauchi ta kori sarakunan gargajiya 6 daga kan karagar mulki bayan gano laifukan da suke aikata wa
  • Hukumar kula da harkokin kananan hukumomi ta ce an tsige sarakunan ne sabida sun shiga siyasa, rashin ɗa'a da sauran saɓa doka
  • A wata sanarwa, hukumar ta umarci su miƙa ragamar mulki hannun sakatarori gabanin naɗa sabbin Sarakuna

Bauchi state - Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin gwamna Bala Muhammed ta tsige Sarakuna 6 daga kan karagar sarauta.

Gwamnatin ta hannun hukumar kula da harkokin kananan hukumomi ta kori sarakunan gargajiya guda 6 ne bisa zargin, "Tsoma baki a siyasa da wasu aifukan rashin ladabi."

Gwamna Bala Muhammed na Bauchi.
Jerin Sunayen Sarakunan da Gwamnatin Bauchi Ta Tsige Kan Zarge-Zarge 2 Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa Sarakunan da suka rasa rawanin sarautar suna karkashin Masarautar Bauchi da kuma Masarautar Katagum.

Matakin tsige Sarakunan na kunshe a wata sanarwa da muƙaddashin babban Sakataren hukumar kula da ƙananan hukumomi, Nasiru Ibrahim, ya fitar a madadin shugaban hukumar.

Kara karanta wannan

"Babu N8,000" Cikakken Jerin Garaɓasa 6 da FG Ke Shirin Raba Wa 'Yan Najeriya Don Rage Raɗaɗi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwan wacce aka raba wa manema labarai a Bauchi, ta ce:

"Hukumar kula da ƙananan hukumomi ta amince da korar sarakunan gargajiya shida a Masarautun Bauchi da Katagum."
"Hakan ya biyo bayan shigarsu cikin harkokin siyasa ta bangaranci, rashin da’a, kwace dazuzzuka ba bisa ka’ida ba, sare itatuwa, da almubazzaranci da dukiyar al’umma da rashin bin doka da oda wanda ya saba wa ka’idar aikin gwamnati."

Jerin Sarakunan da gwamnatin Bauchi ta kora daga karagar mulki

Sanarwan ta bayyana sunaye da muƙaman sarakunan da korar ta shafa a masarautar Katagum, ga su kamar haka:

1. Alhaji Aminu Muhammad Malami - Hakimin Udubo

2. Alhaji Bashir Kabir Umar - Hakimin Azare

3. Umar Omar - Magajin Garin Gadiya

4. Umar Bani - Magajin garin Tarmasawa

Sauran mutum biyu da aka kora a Masarautar Bauchi su ne;

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Uba Sani Ta Gano Sabuwar Cutar da Ta Ɓalle a Kaduna, Ta Faɗi Matakan da Ta Ɗauka

5. Bello Suleman - Magajin garin Beni

6. Alhaji Yusuf Aliyu Badara - Magajin garin Badara.

Sanarwan ta ƙara da umartan dukkan sarakunan da matakin ya shafa su miƙa ragama hannun Sakatarorinsu gabanin naɗa sabbi, Leadership ta ruwaito.

EFCC Ya Gurfanar da Tsohuwar Minista da Wasu 8 Bisa Zargin Wawure N7.9bn

A wani rahoton kuma Hukumar EFCC ta maka tsohuwar ministar sufurin jiragen sama, Stella Oduah gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja.

Ana zargin Stella da haɗa baki da wasu hadiman gwamnati da kamfanoni wajen karkatar da kuɗi kimanin biliyan N7.9.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262