"Ba Zancen N8k" Jerin Kayan Agajin Da Gwamnatin Tinubu Za Ta Raba Wa Yan Najeriya

"Ba Zancen N8k" Jerin Kayan Agajin Da Gwamnatin Tinubu Za Ta Raba Wa Yan Najeriya

  • Majalisar ƙoli ta tattalin arziki a Najeriya ta yanke shawarar matakan da ya kamata a ɗauka domin rage wa yan Najeriya raɗaɗin cire tallafin mai
  • Matakan da NEC ta cimma matsaya a kansu sun haɗa da tallafin kuɗi da kuma alawus ɗin tafiye-tafiya na tsawon watanni 6 ga ma'aikata
  • Har ila yau, gwamnatin Najeriya ta ce zata hanzarta auwatar tsarin canja makamashi, watau sauya motoci daga amfanin da man fetur zuwa Gas

FCT Abuja - Majalisar ƙoli mai kula da harkokin tattalin arziki a Najeriya (NEC) ta amince da ɗaukar wasu matakai domin dakile wahalhalun cire tallafin man fetur ga 'yan Najeriya.

A rahoton Channels tv, NEC ta amince da matakan ne a wurin taron da ta gudanar ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli, 2023 a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Shugaba Tinubu Ya Sake Magana Mai Jan Hankali Kan Matsalar Tsaron Najeriya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
"Ba Zancen N8k" Jerin Kayan Agajin da Gwamnatin Tinubu Zata Raba Wa Yan Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Taron wanda ya gudana karkashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya samu halartar gwamnonin jihohi 36 na Najeriya.

Haka nan kuma darakta janar na ƙungiyar gwamnonin Najeriya, da masu ruwa da tsaki daga bankin duniya da wakilan wasu hukumomi da ma'aikatu sun samu halartar zaman.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mahalarta taron sun cimma matsayar tura wa yan Najeriya tallafin kuɗi ta hanyar amfani da rijistar zamantakewa da walwalar al'umma ta jihohi.

Har ila yau, sun roƙi jami'an gwamnati su rage yawan kashe-kashen kuɗi wajen harkokin shugabanci yayin da gwamnatin tarayya zata bai wa ma'aikata alawus na tsawon wata 6.

Bugu da ƙari, za a raba kayan abinci, hatsi da takin zamani ga gwamnatocin jihohi a farashi mai rahusa daidai da yadda hukumar bada agajin gaggawa (NEMA) ta siya.

Majalisar ta kuma roƙi jihohi da su ɓullo da wasu tsare-tsare domin daƙile tsadar kuɗin tafiye-tafiye.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Uba Sani Ta Gano Sabuwar Cutar da Ta Ɓalle a Kaduna, Ta Faɗi Matakan da Ta Ɗauka

Jerin matakan da NEC ta amince da su

  • Tattauna wa kan sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata
  • Ya kamata kowace jiha ta yi shirin aiwatar da shirin raba wa mutane tallafin kuɗi bisa tsarin rijistar walwala ta jihar.
  • Tsarin tallafin kuɗi na tsawon watanni 6 ga ma'aikatan gwamnati
  • Gwamnatin jihohi su hanzarta biyan ma'aikata albashin da suke bi
  • Ya kamata gwamnati ta fara bai wa kanana da matsakaitan sana'o'i MSMEs bashi mai ƙarancin kuɗin ruwa
  • Gaggauta aiwatar da shirin sauya makamashi, watau canza man da ababen hawa ke amfani da shi daga man Fetur zuwa Gas.

Cire Tallafi: Gwamnatin Tinubu Ta Fara Yunkurin Karya Farashin Kayan Abinci

Rahoto ya nuna cewa nan ba da jimawa ba jihohin Najeriya zasu ga farashin kayayyakin abinci ya faɗi warwas ya dawo daidai aljihun talaka.

Wannan na zuwa ne yayin da majalisar NEC ta umarci hukumar NEMA ta gaggauta fito da hatsi ta raba wa jihohi domin karya farashin abinci.

Kara karanta wannan

Sauƙi Ya Zo: Gwamnatin Tinubu Zata Karya Farashin Abinci a Jihohi, Ta Bada Sabon Umarni Ga NEMA da CBN

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262