Cire Tallafi: Gwamnatin Tinubu Ta Fara Yunkurin Karya Farashin Kayan Abinci
- Nan ba da jimawa ba jihohin Najeriya zasu ga farashin kayayyakin abinci ya faɗi warwas ya dawo daidai aljihun talaka
- Wannan na zuwa ne yayin da majalisar NEC ta umarci hukumar NEMA ta gaggauta fito da hatsi ta raba wa jihohi domin karya farashin abinci
- A cewar gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi, Shettima ya umarci NEMA ta fito da hatsi cikin hanzari domin sauƙaƙa wa yan Najeriya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Majalisar tattalin arziƙi ta ƙasa (NEC) karkashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ta umarci hukumar bada agajin gaggawa ta gaggauta fito da hatsi.
NEC ta umarci hukumar NEMA ta raba wa jihohin Najeriya hatsin cikin mako ɗaya ko biyu masu zuwa domin sauko da farashin kayan binci a faɗin ƙasar nan.
Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ne ya bayyana haka yayin da yake hira da 'yan jarida dangane da abinda suka tattauna a taron NEC ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ne ya jagoranci taron wanda ya gudana a fadar Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shettima ya bai wa NEMA sabon umarni
Kauran Bauchi ya ce Shettima ya umarci NEMA ta gaggauta buɗe rumbunan gwamnati, ta fito da hatsi kuma a cewarsa za a haɗa hannu da jihohi domin sakon ya isa ga talakawa.
Jaridar Daily Trust ta rahoto gwamna Muhammad na nuna damuwa kan tsadar abinci, a cewarsa batun abinci ne babbai abinda majalisar NEC ta maida hankali a zaman.
A kalamansa, Bala Muhammed ya ce:
"Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta tattauna yadda za a ba wa dukkan bangarori da kuma dukkan sassan ƙasar nan tallafi. Abinci shi ne mafi muhimmanci a batun wadata abinci."
"Game da tsadar abinci kuma mun yi farin ciki saboda majalisar ta haɗa kai da NEMA, babban bankin Najeriya da kuma ma'aikatar noma, muna da tarin hatsi a hukumar NEMA."
"Saboda haka majalisar ta umarci hukumar ta raba wa jihohi kyayyakin abinci, hatsi da sauransu domin karya farashin abinci da ya yi tsada. Za a raba waɗan nan kayan abinci a farashi mai rasuha."
Ya ce tsarin bada bashin noma na CBN ya tara tulin shinkafa da sauran hatsi kuma dukkansu NEC ta umarci a rabawa jihohi cikin mako ɗaya zuwa biyu, Punch ta ruwaito.
Tinubu: Sanatan Anambra Ya Musanta Tura Sunayen Ministoci Ga Majalisar Dattawa
A wani rahoton kuma Gaskiya ta bayyana kan raɗe-raɗin da ke yawo cewa shugaba Tinubu ya miƙa sunayen ministoci ga majalisar dattawa.
Sanata mai wakiltar Anambra ta tsakiya, Sanata Victor Umeh, ya bayyana cewa har yanzu sunayen Ministocin shugaban ƙasa, Bola Tinubu ba su ƙarisa majalisar dattawa ba.
Asali: Legit.ng