Yan Bindiga Sun Tsere Yayin da Dakarun Sojoji Suka Kakkabe Dajin Kaduna

Yan Bindiga Sun Tsere Yayin da Dakarun Sojoji Suka Kakkabe Dajin Kaduna

  • Dakarun rundunar sojoji sun fara aikin kakkabe dajin Kaduna bayan samun bayanan sirri kan wasu yan bindiga da ke kokarin kafa sansanoni a yankin Kagarko
  • Yan bindiga sun rasa wurin buya inda suka tattara yanasu-yanasu suka fice daga yankin
  • Sojojin da yawansu ya fi 100 sun isa kauyukan Iche, Taka-Lafiya, Gidan Makeri da Janjala a kewayen dajin don farmakar yan bindigar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kaduna - Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun fara tserewa daga mabuyarsu a garuruwan Kagarko, Iche, Taka-Lafiya Gidan Makeri da Janjala a jihar Kaduna bayan sama da sojoji 100 sun mamaye jejin a karamar hukumar Kagarko.

A yan watanni da suka gabata, garuruwan karkara da dama a masarautar Kagarko sun sha fama da hare-haren yan bindiga wadanda ke sace mazauna da manoma.

Sojoji na kakkabe yan bindiga a Kaduna
Yan Bindiga Da Yan Ta’adda Sun Tsere Yayin da Dakarun Sojoji Suka Kakkabe Dajin Kaduna Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Sai dai kuma, an tattaro cewa lamarin ya yi sauki bayan dakarun sojoji sun farmaki mabuyansu da wasu garuruwan karkara sannan suka kama wasu da ake zaton masu kai masu kwarmato ne.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Ragargaji Yan Ta’adda Ta Sama, Sun Kashe Mayaka 22 Masu Biyayya Ga Marigayi Abdulkareem Boss

Sojojin sun tafi dajin Kaduna kai tsaye domin kakkabe yan bindigar

Zagazola Makama ya rahoto cewa wani basarake a Kagarko, Suleiman Aliyu, ya bayyana a ranar Laraba, cewa dakarun wadanda suka shigo garin Kagarko da misalin 11:00 na safiyar Laraba a cikin motar Hilux, manyan motoci da babura, sun tafi kauyukan Iche, Taka-Lafiya, Gidan Makeri da Janjala a kewayen dajin kai tsaye don farmakar yan bindigar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce dakarun sojin sun shigo garin bayan sun samu bayanan sirri cewa wasu yan bindiga da ke tserewa daga yankin arewa suna dawowa yankin don kafa sansanoni a wasu kauyukan da ke yankin.

Da yake yaba ma kokarin sojojin, Aliyu ya bayyana cewa tun bayan kama wasu masu kaiwa yan bindigar bayanai mazauna masarautar Kagarko sun samu sauki.

Wata majiya daga fadar sarkin Kagarko, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta fada ma Zagozola Makama cewa:

Kara karanta wannan

Jami’an ‘Yan Sanda Sun Damke Daya Daga Cikin Mutanen Da Ke Da Hannu Wajen Kashe Babban Dan Siyasa

"Eh; wasu dakarun sojoji masu yawa sun shiga dajin a yau, da nufin kakkabe mabuyar yan bindigar."

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna ba a kan lamarin a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Sojoji sun halaka mayakan ta'addanci 22 a jihar Katsina

A wani labarin kuma, dakarun rundunar sojin sama sun yi barin wuta a kan yan ta’adda a jihar Katsina inda suka murkushe mayaka 22.

Yan ta’addan da aka halaka sun kasance masu biyayya ga marigayi Abdulkareem Boss wanda sojoji suka halaka a bara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel