"Tana Rayuwa a Shekarar 3023": Wata Mata Ta Tuka Amala Da Na'ura Maimakin Muciya

"Tana Rayuwa a Shekarar 3023": Wata Mata Ta Tuka Amala Da Na'ura Maimakin Muciya

  • Wani bidiyo da ke nuna wata mata tana tuka Amala a kan wuta da na'urar zamani ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
  • Matar ta rike na'urar yayin da take zaune a gaban katon tukunya inda ta dunga juya amalar cikin sauri
  • Mata da dama da suka yi martani ga bidiyon sun ce a karshe sun samu mafita na yin amala cikin sauki

Wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuno lokacin da wata mata ta yi amfani da na'ura wajen tuka amala a katon tukunya.

Ta tura na'urar mai kama da maburgi a cikin amalar da ke kan wuta inda ta dungi juya shi da kyau.

Matar t yi amfani da na'ura wajen tuka amala
"Tana Rayuwa a Shekarar 3023": Wata Mata Ta Tuka Amala Da Na'ura Maimakin Muciya Hoto: @platinumamalaspot
Asali: TikTok

Matar TikTok ta yi amfani da na'ura wajen tuka Amala

Bayan matar @platinumamalaspoy ta yi amfani da na'urar wajen tuka amalar, sai ta koma ga muciya wajen jujjuya shi don gudun kada ya yi gudaji.

Kara karanta wannan

An Yi Son Kai: Majalisa Za Ta Binciki Duka Mukaman da Aka Bada a Mulkin Buhari

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutane da dama da suka kalli bidiyon sun yi magana kan yadda wannan dabarar ya dace a wajen girka Abinci.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit.ng ta tattara wasu martanin jama'a a kasa:

Tamilola ta ce:

"Na sani cewa bai kamata tuka Amala ya dauki tsawon rayuwar mutum ba. Na so wannan sabon dabarar."

Khalisea ta ce:

"Idan wadannan matan ne suke tuka amalan, zan ci shi."

Queen_daniai ta ce:

"Za mu samu da sauki idan muka yi aure ni da nake da maburgi da dama, mijina ma zai hada hannu da ni wajen burga amala."

HennySwitch ta ce:

"Yanzu gidan miji zai yi sauki don Allah na shirya aure."

temmy5555 ta ce:

" Zan dunga amfani da karamin maburgija wajen tuka amala kenan."

Emiloju ta ce:

"Watakila zan iya yin amala da kyau da wannan abun. "

Kara karanta wannan

Malamin Addini A Najeriya Ya Magantu Kan Zargin Aiki Da Kwankwamai A Majami'arsa

Magidanci na shirin auren uwar matarsa da ta mutu

A wani labari na daban, mun ji cewa wani mutum ya bayyana aniyarsa na son auren mahaifiyar matarsa da ta mutu ta bar masa yara uku.

A cewar mutumin, ya zabi auren surukar tashi ne maimakon ya je ya dauko wata daga waje da za ta zo ta muzgunawa yaransa ko ma ta raba kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng