“Ina Mai Ba Da Hakuri”: A Karshe Mmesoma Ta Ba Hukumar JAMB Hakuri
- Ejikeme Mmesoma, yarinyar da ta kirkiri sakamakonta na UTME ta nemi afuwar hukumar JAMB
- Mmesoma ta sauya makin da ta samu a UTME daga 249 zuwa 362, tana mai ikirarin cewa ita ta fi kowa yawan maki a 2023, amma sai aka gano karya ne
- Yanzu ta ba hukumar JAMB hakuri, tana mai neman ayi mata sassauci domin wannan shine karo na farko da take aikata haka
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Dalibar nan mai shekaru 19 wacce hukumar shirya jarabawar shiga jami’a (JAMB) ta zarga da kirkirar sakamakon jarrabawarta na UTME, Mmesoma Ejikeme, ta ba hukumar hakuri a kan abun da ta aikata.
Mmesoma ta karanto wani wasika na ban hakuri a yayin zaman sauraron rahoton kwamitin bincike da majalisar wakilai ta kafa domin bincikar lamarin karkashin jagorancin Sada Soli.
A wani bidiyo da jaridar TheCable ta wallafa a Twitter, Mmesoma ta ce abun da ta aikata ba daidai bane sannan ta nemi a yafe mata.
Matashiyar ta nemi ayi mata sassauci yayin da ta dauki alkawarin cewa irin abu haka ba zai sake faruwa ba, jaridar The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta kuma bayyana cewa bata taba satar amsar jarrabawa ba a tsawon rayuwarta.
Daga cikin wadanda suka halarci zaman sauraron lamarin harda shugaban hukumar JAMB, Farfersa Isiaka Oloyede.
Mafarin shiga matsalar Mmesoma
Mmesoma ta shahara ne bayan ta yi ikirarin cewa ta samu maki 362 a jarrabawarta na UTME na 2023.
Amma da aka fara bincike, JAMB ta ce Mmesoma bata samu maki 362 ba maimakon haka maki 249 ta samu. Hukumar ta ce ta kirkiri sakamakonta.
Bayan gwamnatin Anambra ta kafa kwamitin bincike a kan zargin da ake yi mata na kirkirar sakamakon, sai aka gano gaskiya ne sannan aka nemi ta ba JAMB hakuri.
A jawabinta na ban hakuri, Mmesoma ta ce:
“Na rigada na yarda cewa abun da na aikata ba daidai bane. Ina mai bayar da hakuri a kan duk wadanda aka daurawa laifi da kuma radadin da na haddasa. Rashin sani ya taka muhimmiyar rawa a kan abun da na aikata. Wannan shine karo na farko da nake yin haka a rayuwata da kuma bangaren karatu da za a zarge ni da rashin da’a. Ba dabi’a ta bace kuma ba hali na bane. Saboda haka, ina neman sassauci.”
Kalli bidiyon a kasa:
Mmesoma ta sharbi kuka kan abun da ta aikata, ta sha alwashin ba da hakuri
A baya Legit.ng ta rahoto cewa wani sananne kuma mai bayar da agaji, Harrison Gwamnishu, ya yi wani ɗan ƙaramin bidiyo inda ya roƙi ƴan Najeriya da su dai na caccakar Mmesoma Ejikeme.
Mutumin ya bayyana cewa ya samu kiran gaggawa ne daga yarinyar, inda ta yi niyyar yi wa kanta illa saboda ƙarin makin da ta yi domin ba za ta iya fuskantar abun kunyan da ta yi ba.
Asali: Legit.ng